'Sun Gane Kuskurensu,' An Bankado Shirye Shiyen Atiku da Obi a kan Zaben 2027
- Wani makusancin Atiku Abubakar ya ce tattaunawar sirri tsakanin abokinsa da Peter Obi domin su hada karfi su fitar da Bola Tinubu daga ofis
- Majiyar ta ce Atiku da Obi sun fahimci cewa hadin guiwa ce kadai mafita don cimma nasarar shugabanci nagari tare da ceto Najeriya
- An zargi Shugaba Tinubu da kokarin raba kawunan 'yan Arewa da na Kudu domin samun rinjayen kuri'un 'yan kasa a zaben shekarar 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani aminin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Atiku na da niyyar hada kai da Peter Obi, domin su kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Majiyar ta bayyana cewa dukkanin jagororin za su iya jawo Tinubu ya rasa kujerarsa matukar suka yi aiki tare a kakar zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
Obi, Okowa da mutanen da Atiku ya jawo jiki, amma suka fice daga PDP suka bar shi

Source: Facebook
A cewar majiyar, wadda ta bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch, Atiku da Obi sun gane cewa ba za su iya cimma burin shugabanci nagari a Najeriya ba sai sun hada kai.
Tinubu: Atiku Abubakar zai yi aiki da Peter Obi
Majiyar ta kara da cewa wannan dalili ne ya sa suka yanke shawarar fara aiki tare, duk da cewa har yanzu ana tattaunawa cikin sirri.
Ta ce:
“Babu tantama cewa sun koyi darasi kuma a shirye suke su yi aiki tare. Sun gane cewa ba za su kayar da Tinubu a daidaikunsu ba."
“Binciken sakamakon zaben 2023 ya nuna cewa Atiku ya lashe jihohi 12 tare da sama da kuri’u miliyan shida, yayin da Obi ya lashe jihohi 11 da kuma Babban Birnin Tarayya.
“Idan aka hada kuri’un su, za su zarce kuri’u miliyan takwas da Tinubu ya samu. Wannan ne ya sa ake gudanar da muhimman taruka tsakanin bangarorin biyu, kodayake ana yi ne cikin sirri.”
Ana zargin Tinubu da raba kan kasa
Majiyar ta kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kokarin raba kan yankin Arewa da Kudancin Najeriya domin samun nasara a zaben gaba.
Ta ce wannan mataki na daga cikin abin da ya haifar da ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, daga tafiyar shugaban kasa.

Source: Facebook
A cewarta:
“Tinubu na kokarin haddasa rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu, yana zaton hakan zai taimaka masa wajen kafa hadakar da za ta ba shi nasara. Amma wannan kuskure ne– wannan ne ma daya daga cikin dalilan da suka sa El-Rufai ya fice.”
Yadda Atiku ya rasa makusantansa
A baya, mun wallafa cewa wasu daga cikin kusancin abokan siyasar Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP, sun fice daga jam’iyyar duk da yana cikinta har yanzu.
Daga cikin wadanda suka fice daga jam'iyyar akwai tsofaffin abokan takararsa, Peter Obi da Ifeanyi Okowa, sai kuma wadanda suka yi masa kamfe, kamar Gbenga Daniel da Daniel Bwala.
Daga cikin makusantansa da suka fice daga jam'iyya, wasu sun koma yiwa gwamnati mai ci aiki, yayin da a halin da ake ciki, Atiku ke kokarin hada kai da Obi domin samun nasara a zaben gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
