Uwar Bari: Fubara zai Kara Zama da Wike a Shirin Sulhu a Rivers, APC da PDP Sun Magantu

Uwar Bari: Fubara zai Kara Zama da Wike a Shirin Sulhu a Rivers, APC da PDP Sun Magantu

  • Gwamna Simi Fubara da tsohon ubangidansa, Nyesom Wike, sun fara tattaunawar sulhu domin kawo karshen rikicinsu
  • Tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba, da na yanzu, Dapo Abiodun, ne suka jagoranci sasancin da aka fara a Abuja
  • Ana sa ran Fubara da Wike za su sake haduwa nan gaba domin kammala cikakkiyar yarjejeniyar sulhu a jihar Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Bayan dogon lokacin rikicin siyasa a jihar Ribas, an fara wani sabon yunkuri na sasanci tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Simi Fubara wanda ke cikin rikici da tsohon ubangidansa a siyasance, ya gana da Wike a Abuja cikin wani yunkuri na warware sabanin da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi bayan kisan fitinannen ɗan bindiga da ya addabi Arewa

Fubara
Fubara zai sake zama da Wike. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Ezonwo Wike
Source: Facebook

Rahotanni daga jaridar Punch sun tabbatar da cewa an samu ganawar sirri tsakanin bangarorin biyu a gidan Wike da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fubara zai sake zama da Wike

Ana sa ran za a sake wani zama nan ba da jimawa ba domin kammala shirin sulhun da ke da nufin kawo zaman lafiya a jihar Ribas.

Hakan na zuwa ne bayan shiga tsakani da tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba, da kuma gwamna mai ci, Dapo Abiodun suka yi.

Ganawar Fubara da Wike ta farko a Abuja

Wani da ya halarci ganawar ya bayyana cewa an yi dogon tattaunawa tsakanin shugabannin biyu, inda Fubara ya nemi gafarar Wike kan abubuwan da suka faru a baya.

Premium Times ta bayyana cewa gwamna Fubara ya durƙusa tare da roƙon Wike gafara a gaban gwamnonin Ogun biyu.

Tun bayan kammala zaben 2023 ne aka fara samun sabani tsakanin Wike da Fubara, wanda hakan ya janyo rikicin siyasa da ya daɗe yana girgiza jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Portable: Bayan zayyano laifuffukansa, kotu ta tura fitaccen mawaki gidan kaso

Jigon PDP ya ba Fubara shawari kan sulhun

Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya shawarci Fubara da kada ya bar sulhun ya shafi muradun al’ummar jihar.

Timothy Osadolor ya ce:

“Ko da sulhu na girmamawa ne, bai kamata Fubara ya sadaukar da muradun al’ummar Rivers ba don rufa wa kansa asiri.”

APC ta yaba da zaman sulhun da aka fara

A wani bangaren, jam’iyyar APC ta bayyana jin daɗinta bisa rawar da shugabanninta suka taka wajen wannan sulhu.

Daraktan yada labarai na jam’iyyar, Bala Ibrahim, ya ce wannan mataki na nuna cewa APC na da kishin kasa da zaman lafiya.

Bala Ibrahim ya ce:

“Wannan ba siyasa ba ce, sai dai ƙoƙari na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Ribas,”

Bala Ibrahim ya kara da cewa:

“APC na goyon bayan duk wani yunkuri da zai kawo ci gaba da daidaito a kowace jiha.”

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Yadda gwamna Fubara ya tsuguna a gaban Wike ya nemi gafara

Ana sa ran ci gaba da wannan tattaunawa zai taimaka wajen dakile rikicin siyasar da ya dade yana hana cigaba a jihar Ribas.

Fubara
APC ta yaba da zaman sulhu da aka fara tsakanin Fubara da Wike. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike|Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Fubara ya gana da Tinubu a London

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers da aka dakatar ya gana da Bola Tinubu a birnin London kwanan nan.

An ruwaito cewa ganawar na da alaka da rikicin jihar Rivers da ya jawo dakatar da gwamna Simi Fubara daga ofis.

Duk da cewa ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba, an ce ganawar na da alaka da duba yiwuwar dawo da Fubara ofis kafin wata shida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng