Gwamnan PDP Ya Saba da Jam'iyyarsa, Ya Nuna Goyon baya ga Tazarcen Tinubu a 2027
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya nuna goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu domin samun wa’adin mulki na biyu
- Mai girma Umo Eno ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da aikin titin Legas zuwa Calabar da ya ratsa sashen jihar Akwa Ibom
- Gwamna Eno ya bayyana cewa ayyukan samar da ababen more rayuwa Tinubu da ke yi, sun taimaka wajen samun ci gaba a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom na jam'iyyar PDP, Umo Eno, ya yi magana kan makomar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na jam'iyyar APC zai kwashe shekara takwas yana mulki a Najeriya.

Asali: Facebook
Gwamna Umo Eno ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙaddamar da aikin titin Legas zuwa Calabar na sashen jihar Akwa Ibom a ranar Talata, 15 ga watan Afirilun 2025, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan
2027: Sanatan APC ya tabo batun tazarcen Gwamna Namadi, ya ba 'yan siyasa shawara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnan Akwa Ibom ya ce kan Tinubu?
Uno Eno ya yabawa shugaban ƙasan kan aikin titin da ya fara yi, ya ce zai kammala shi tare da ƙaddamar da shi da hannunsa, rahoton PM News ya tabbatar.
Gwamnan ya bayyana cewa za su ci gaba da mara baya ga shugaban ƙasan domin ci gaba da gudanar da ayyukan da yake yi.
"Bari na kammala da tabbatarwa shugabanmu (Tinubu), shugaban da ke ƙaunar jama’a, cewa zai kammala shekara takwas, domin za mu mara masa baya. Wannan shi ne gaskiya ne."
“Ba zai fara wannan aiki ba (aikin titin gaɓar teku daga Legas zuwa Calabar) sannan wani mutum daban ya zo bai kammala ba."
"Addu’ar mu ga shugaban ƙasa ita ce Allah ya ba shi lafiya mai ɗorewa domin kammala aikin da ya fara, ya ƙaddamar da shi, domin ka da a manta da aikin."
"Ka da ya zama kamar titin hanyar Gabas da Yamma. Wannan aikin zai kammalu, hannun da ya fara shi ne zai kammala shi da sunan Yesu.
- Gwamna Umo Eno
Gwamna Eno ya sha alwashi kan Tinubu
Gwamnan na jihar Akwa Ibom ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Twitter
Ya ce shugaban ƙasan ya yi aiki tare da su duk da cewa akwai bambancin jam'iyya a tsakaninsu.
Gwamnan ya yi alƙawarin mayar da biki saboda irin ɗumbin ayyukan alherin da shugaban ƙasan ya yi musu.
"Shugaban ƙasa ya nuna mana ƙauna kuma yana yin aiki tare da mu duk da cewa akwai bambancin jam’iyya."
“Za mu ci gaba da yin aiki tare da shi domin yaɗa labaran ci gaba, zurfafa haɗin kai, imani, da alfaharin kasancewarmu ƴan Najeriya."
- Gwamna Umo Eno
An shirya gangamin nuna goyon bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa matasan yankin Kudu maso Gabas sun shirya gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Sanata Uzor Orji Kalu.
Ƙungiyar matasan yankin Kudu maso Gabas (COSEYL) ita ce ta shirya gangamin na mutum miliyan biyar domin nuna goyon bayansu ga ƴan siyasan kan zaɓen 2027.
Matasan dai waɗanda za su fito daga jihohi biyar na yankin, za su yi gangamin ne domin tallata ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu ke yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng