An Kaure tsakanin Ƴaƴan Atiku da Gwamna Bala kan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Rikici ya barke tsakanin yaron Atiku Abubakar da ɗan gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, kan batun takarar shugaban ƙasa a 2027
- Ɗan Atiku ya zargi Bala da kin tallafa wa mahaifinsa a zaɓukan 2019 da 2023, duk da rike shugabancin tawagar goyon bayan Atiku a PDP
- Shamsudeen Bala ya ce mahaifinsa ba zai sake mara wa Atiku baya ba, saboda Atiku ya nemi hana a sake zaɓen gwamnan Bauchi a 2023
- Mohammed Abubakar ya ce Bala na aiki a asirce da gwamnatin Tinubu kuma ya na amfani da burin shugabancin ƙasa wajen ɓata lamarin PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wata mahawara ta ɓarke tsakanin ‘ya’yan Atiku Abubakar da gwamnan Bauchi Bala Mohammed.
Rigimar ta barke ne kan burin iyayensu na shugabancin ƙasa a zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan
'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027

Asali: Facebook
Musabbabin rigimar ɗan Atiku da yaron Bala
Punch ta ce ɗan Atiku, Mohammed Abubakar, ya zargi Gwamna Mohammed da kin tallafa wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa a zaɓukan 2019 da kuma 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed wanda ke jagorantar ƙungiyar masu goyon bayan Atiku, ya ce burin Bala na zama shugaban ƙasa na haddasa rikici a cikin jam’iyyar PDP.
Ɗan Atiku ya mayar da martani ne ga maganganun ɗan gwamnan Bauchi, Shamsudeen Bala, wanda ya ce mahaifinsa ba zai sake goyon bayan Atiku ba.
A ranar Juma’a, Shamsudeen Mohammed ya zargi Atiku da hana nasarar sake zaɓen mahaifinsa a 2023 ta hanyar haɗa kai da ‘yan adawa a jihar Bauchi.
“Gaskiya, zai zama da wahala, Ko ya ci zaɓe, ba zai yi mana komai ba illa ɗaukar fansa, bai taimake mu a 2023 ba.”
“Ya goyi bayan ɗan takarar APC kuma ya haɗa kai da manyan ‘yan Bauchi don kayar da mu, mun sha wuya kafin mu tsira."

Kara karanta wannan
"Karshen PDP ya zo," George ya hango abin da zai faru idan aka ba Atiku takara a 2027

Asali: Facebook
Ɗan Atiku ya soki yaron Gwamna Bala
A martanin da ya fitar a ranar Litinin, ɗan Atiku ya zargi Gwamna Bala da aiki a asirce da APC da gwamnatin Bola Tinubu.
“Shamsu ya sani, Atiku bai taɓa shiga matsalolin siyasar mahaifinsa ba, Atiku ba ya shiga irin waɗannan hargitsi.”
Ya ƙara da cewa duk wata matsala da Bala ya fuskanta kafin zaɓen 2023 ta faru ne a cikin gida, ba tare da alaƙa da Atiku ba.
Ya kara da cewa:
“A kowane lokaci, mahaifin Shamsu bai taɓa goyon bayan Atiku a siyasa ba, a 2023 ma, ya yi wa Atiku zagon ƙasa.”
Ɗan Atiku ya ambato wani jawabi na Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya ce Bala ya yi ƙoƙarin ɓata ƙoƙarin Atiku a 2023.
A cewarsa, burin Bala na zama shugaban ƙasa ya raunana jagorancinsa a cikin kungiyar gwamnonin PDP kuma ya lalata haɗin kai.
“Muna da labarin hulɗarsa a asirce da gwamnatin Tinubu."
- Cewar ɗan Atiku
Atiku ya soki matakin PDP kan haɗaka
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dage cewa dole ne a hada kai don a karbe mulki daga Bola Tinubu a 2027.
Atiku ya ce wannan yunkuri mallakin jama’a ne, kuma yana da karfin da zai ci gaba har sai gwamnonin sun fahimta kuma sun hada kai.
Gwamnonin PDP guda 11 sun nesanta kansu daga hadin gwiwa da Atiku ke kokarin yi tare da sauran shugabannin hamayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng