Atiku: Gwamna Ya Fadi Dalilin Gwamnonin PDP na Watsi da Kawancen Jam'iyyu
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba ta da niyyar shiga haɗaka da wasu ’yan adawa a zaɓen 2027
- Bala Mohammed ya ce PDP tana da gwamnoni 12 da sauran manyan shugabanni a matakai daban-daban, hakan ya sa ba su ga dalilin shiga wata hadaka ba
- Sanata Bala ya ce babu wani dalili da zai sa PDP ta sauya tafiya ko shiga sabuwar kawance, domin ba su aikata wani kuskure ba da zai sa su fice daga jam’iyyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed ya nesanta jam'iyyar da yunƙurin Atiku Abubakar na hade wa da wasu ’yan adawa gabanin zaɓen 2027
Ya bayyana cewa sun samu labarin Atiku Abubakar na kokarin samar da kawancen jam’iyyu, amma bai tuntubi jam’iyyar a hukumance ba.

Kara karanta wannan
'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Bala Mohammed ya bayyana cewa ba su da ra’ayin barin PDP su shiga wata haɗaka da wasu ’yan adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce PDP ta kai matsayi da girma wanda ya fi dacewa da a nemi shiga cikinta, maimakon ita ta je ta nemi haɗaka da wasu, musamman don fuskantar gwamnatin Bola Tinubu a 2027.
Dalilin gwamnonin PDP na watsi da hadakar Atiku
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya ce PDP tana da gwamnoni, ’yan majalisar tarayya, ’yan majalisun jihohi, shugabannin kananan hukumomi da sauran masu madafun iko a Najeriya.
Ya ce:
“Ba za mu bar jam’iyyarmu, inda muke da gwamnoni 12, da Sanatoci, da ’yan majalisun jiha, da Kansiloli da Ciyamomi, mu je mu shiga jam’iyyar da ba ta da ko kansila ɗaya ba.”
“Babu wani nasaba, babu wani haɗin kai, kuma ba mu da wani ra’ayi na barin jam’iyyarmu mu shiga wata.”
Sanata Bala Mohammed ya ƙara da cewa babu wani laifi da PDP ta aikata da zai sa su yanke hukuncin shiga hadakar jam’iyyu. Saboda haka, ba su da wani dalili na sauya tafiya.

Asali: Facebook
Fatan gwamnonin PDP ga Atiku Abubakar
Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya ƙara da cewa sun san da yunƙurin Atiku Abubakar na shiga haɗakar jam’iyyu don tunkarar zaben 2027, amma bai yi shawara da su ba.
Ya ce:
“Bai taɓa tambayarmu ba, bai tuntubi jam’iyya ba. Mun san yana da yancinsa, kuma yana da kima da zai yi abin da ya ga dama. Amma mu ba inda za mu je; muna inda muke da jam’iyya. Kuma muna yi masa fatan alheri.”
‘Gwamnonin PDP ba su matsawa Atiku ba,’ Dingyadi
A ƙarin bayani da ya yi wa Legit, Yusuf Dingyadi, mashawarcin mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, ya bayyana cewa gwamnonin PDP ba su ƙi haɗakar jam’iyyu saboda kiyayya ba.
Ya ce:
“Wannan magana ta kai kusan shekaru huɗu ko biyar ana cewa PDP ba za ta yi haɗaka ba. Wannan ba sabon abu ba ne; yanzu ne dai aka fito fili aka tabbatar da matsayar.”
“PDP tana daga cikin jam’iyyun da suka fi dadewa a Najeriya, kuma rashin shiga haɗakar wata jam’iyya ko sauya suna ba laifi ba ne.”
Atiku ya saba da gwamonin PDP
A baya, mun wallafa cewa Atiku Abubakar, ya bayyana rashin amincewar gwamnonin PDP da shirin kafa kawance a matsayin barazana ga nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Atiku Abubakar, ta bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe ya bayyana cewa haɗin gwiwa ce kadai hanyar da za ta iya fitar da Bola Ahmed Tinubu daga mulkin kasar nan .
Atiku ya soki matsayar gwamnonin PDP a karkashin gwamnan Bauchi, Bala Mohammed yana mai cewa Najeriya na bukatar haɗin kan 'yan adawa domin fuskantar jam’iyya mai mulki a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng