"Karshen PDP Ya Zo," George Ya Hango Abin da Zai Faru idan Aka ba Atiku Takara a 2027
- Bode George ya yaba wa gwamnonin PDP bisa matakin da suka ɗauka na nesanta kansu da haɗakar jam'iyyun adawa karkashin Atiku Abubakar
- Jigon PDP ya bayyana cewa idan jam'iyyar ta sake kuskuren ba tsohon matainakin shugaban kasar takara, to karshenta ya zo
- George ya ce a tsarin dokokin PDP, Atiku ba shi da damar neman takarar shugaban kasa sai 2031
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan kwamitin amintattun PDP (BoT), Cif Bode George, ya bayyana cewa PDP ta kashe kanta matukar ta sake ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tikiti a zaben 2027.
George, babban kusa a PDP ya jaddada cewa jam'iyyar ba za ta kai labari ba a zaɓen 2027 idan ta sake yin kuskuren tsaida Atiku takarar shugaban ƙasa.

Asali: Twitter
Ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta mutu idan ta sake ba Atiku takara
Bode George ya ce Atiku ya gaza tabbatar wa duniya cewa shi ne jagoran PDP saboda ya kasa kashe wutar rikicin da ya ƙi ci ya ki cinyewa.
Jigon ya ce:
“Idan (Atiku) ya samu tikitin takarar PDP, ku ɗauka ƙarshen jam’iyyar ya zo. Idan ya samu tikitin ta hanyar magudi kamar yadda aka yi a baya, ba za mu amince da hakan ba.”
Atiku, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin PDP a 2023, ya zo na biyu bayan Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jima yana fafutukar neman zama shugaban ƙasa kusan shekaru 30, inda ya tsaya takara sau shida a jam’iyyu daban-daban.
Ƴan adawa sun fara yunkurin haɗaka
A baya-bayan nan, Atiku ya jagoranci ƙirƙirar wata hadakar jam’iyyun adawa a ranar 20 ga Maris, 2025, tare da tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi; tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake gamuwa da matsala a yunƙurinsa na ƙwace mulki daga hannun Tinubu a 2027
Hadakar na da niyyar kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaben 2027, musamman bisa zargin gazawa wajen tafiyar da mulkin ƙasar nan.
Sai dai a wani sabon mataki, gwamnonin PDP sun fito fili a ranar Litinin, 14 ga Afrilu, 2025, suka ki amincewa da hadakar jam’iyyun da Atiku ke jagoranta.

Asali: Twitter
Atiku ya gaza warware rikicin PDP
Bode George ya yabawa gwamnonin bisa wannan matakin, yana mai cewa Atiku bai nuna cewa shi ne jagoran jam’iyyar tunda bai iya sasanta rikice-rikicen cikin gida da ke damun PDP ba.
“Da shi ne jagora na gaske, da ya tsoma baki a rikicin jam’iyyar. Samun tikitin takara a baya ba yana nufin ka zama kai ne jagoran PDP ba,” inji shi.
A lokacin da aka tambaye shi ko Atiku Abubakar na da damar sake tsayawa takara a PDP, George ya ce:
“Ba zai yiwu ba, Arewa ta yi shekaru takwas a mulki yanzu lokaci ne na kudu. Wannan shi ne tsarin dokar PDP. Ba zan ce ba shi da ikon takara ba amma sai dai ya tafi wata jam'iyyar.
Wani ɗan PDP kuma mai goyon bayan Atiku, Kabir Dogo ya shaidawa Legit Hausa cewa abin da gwamnonin jam'iyyar suka yi bai dace ba.
A cewarsa, yana ganin da zama da Waziri suka yi domin jin ta bakinsa kan wannan haɗaka kafin su ɗauki duk matakin da suka ga dama.
"Ni a ganina, ba haka ya kamata gwamnoninmu su yi ba, eh ta yiwu ba a gaya masu batun maja a hukumance ba, amma da shirya taro suka yi da Atiku da ya fi.
"Yanzu sun yanke wannan mataki, ina ganin wataƙila da sun ɗan jinkirta sun ji ta bakinsa, da ba su yanke wanna shawara ba," In ji Kabir.
An bukaci Atiku ya haƙura da takara
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban APC na kasa shiyyar Arewa maso Yamma, Garba Datti Muhammad ya buƙaci Atiku ya haƙura da takara a 2027.
Ya kuma buƙaci tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi sasamtawa da jam’iyyar APC sannan ya koma cikinta.
Garba Datti, ya yi wannan kiran ne a cikin wata budaddiyar wasika da ya aika wa tsohon dan takarar shugaban kasar da Malam Nasir.
Asali: Legit.ng