APC Na Ragargazar 'Yan Adawa a Kano, Barau Ya Karbi Shugabannin Jam'iyyar Hamayya
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karɓi shugabannin jam’iyyar ADP da suka sauya sheka zuwa APC
- Daga cikin mutanen da ya karba akwai shugaban ADP na Gwarzo, Alhaji Nazifi Hassan Gwarzo, da manyan 'yan takarar jam'iyyar a 2023
- Sanata Barau ya bayyana cewa a dalilan jagororin na sauya sheka, sun ce akwai yadda APC ta dage wajen samar da ci gaba a fannoni da dama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sabuwar guguwar sauyin siyasa ta kunno kai a Kano yayin da manyan jagororin ADP na karamar hukumar Gwarzo suka sauya sheka zuwa APC.
Wannan sauyin sheka yana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan siyasa ke ta canza jam’iyya a sassa daban-daban na ƙasar, yayin da shiri-shirin zaɓen 2027 ke kara ɗaukar zafi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Manyan ƴan adawa na shirin haɗaka, ɗan majalisa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP

Asali: Facebook
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ne ya bayyana karbar manyan ADP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 9 ga Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan ADP sun shiga APC ta hannun Barau Jibrin
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Barau ya bayyana cewa ya karɓi bakuncin Alhaji Nazifi Hassan Gwarzo, shugaban jam’iyyar ADP a karamar hukumar Gwarzo.
Sai kuma Saidu Ibrahim, jagoran jam’iyyar a yankin tare da sauran 'yan tawagar gidansa da ke Abuja da safiyar ranar Talata.

Asali: Facebook
Ziyarar ta kuma haɗa da wasu tsofaffin ‘yan takarar jam’iyyar ADP a zaɓen 2023 kamar su Hon. Nazifi Suleiman, dan takarar Kabo/Gwarzo a Majalisar Tarayya da Barista Musa Haruna Yawale, dan takarar Gwarzo a Majalisar jiha..
APC: Barau ya yi maraba da ‘yan ADP
Sanata Barau ya bayyana cewa sababbin ‘yan jam’iyyar sun ce goyon bayan da APC ke bayarwa a fannonin ci gaban ƙasa da shirye-shiryen raya kasa ne suka janyo hankalinsu zuwa jam’iyyar.
Ya ce:
“Sun bayyana cewa yadda APC ke gudanar da ayyuka da tsare-tsare a fannoni daban-daban ne ya ja hankalinsu zuwa APC, wacce ita ce babbar jam’iyya a nahiyar Afirka."
Sanata Barau ya tarbi sababbin ‘yan jam’iyyar da hannu biyu-biyu tare da tabbatar musu da cewa za a ba su cikakken ‘yanci da adalci kamar sauran ‘ya’yan jam’iyya.
Ya kara da cewa:
“Na tabbatar musu cewa kamar yadda muka yi da sauran wadanda suka sauya sheka, za a yi musu adalci. APC jam’iyya ce mai faɗi da ke da damar karɓar kowa,” in ji shi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi kira ga sababbin ‘yan jam’iyyar da su hada kai da APC wajen fuskantar manyan ƙalubalen da ke fuskantar jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Barau ya karbi 'yan SDP zuwa jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji yadda Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar SDP da suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Wadanda suka sauya sheka sun hada da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaben 2023, Yusuf Buhari, da ɗan takarar gwamnan Kano, Bala Muhammad Gwagwarwa.
Sanata Barau Jirbin ya bayyana cewa ya karɓi sababbin ‘yan jam’iyyar APC ne a wani taro mai armashi da aka gudanar a Otal ɗin REIZ Continental da ke birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng