'Arewa Ta Hada Kai da Kudu Maso Gabas': An Ji Dabarar Kwace Mulki daga Hannun Tinubu
- Ibrahim Moddibo, ɗan jam’iyyar SDP, ya ce ana iya kayar da Bola Tinubu a 2027, ba kamar yadda wasu ke ganin rashin yiwuwar hakan ba
- Ya yi nuni da cewa a 2023, Arewa ce ta taimaka wa Tinubu ya ci zabe, amma yanzu mutanen shiyyar ne ke shan wahalar mulkinsa
- Maikudi ya kuma bayyana cewa yanzu ne lokacin da Arewa da Kudu maso Gabas za su haɗa kai, su kayar da Tinubu a babban zaben 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Yayin da zaben shekarar 2027 ke ci gaba da gabatowa, an ba 'yan adawa shawarar kwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu.
Wani matashi, Ibrahim Modibbo Sanusi Maikudi, dan jam'iyyar SDP, ya nuna cewa za a iya kayar da Tinubu a 2027, sabanin tunanin wasu na cewa ba za a iya ba.

Kara karanta wannan
An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Asali: Twitter
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 6 ga watan Afriku, Ibrahim Maikudi ya ce bai kamata a rika yaudarar mutane da cewa Tinubu ya fi karfin ya fadi zabe ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kawo dabarar kayar da Tinubu a 2027
Matashin ya ce ko a zaben 2023 da ya gabata, Shugaba Tinubu bai iya samun nasarar lashe zabe a jiharsa ko yankinsa ba.
A cewar Ibrahim Maikudi, shiyyar Arewa ce ta ba Tinubu nasara da kashi 65% na kuri'un da aka kada a zaben, amma kuma yanzu Arewa ke shan wahalar mulkinsa.
Sakamakon wannan wahalar da ake fuskanta, matashin ya ke ganin cewa Arewa za ta hada kai da Kudu maso Gabas domin kayar da Tinubu a 2027.
Sakon da Ibrahim Modibbo ya wallafa na cewa:
"Kada a ruɗe ku — za a iya kayar da BAT (Bola Ahmed Tinubu). Ya ci shugaban ƙasa da ƙanƙanin rinjaye mafi ƙanƙanta a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan
An bar kasa ba kowa: Shettima ya shilla kasar waje bayan Tinubu ya kwana a Faransa
"Bai iya lashe jiharsa ba, balle shiyyarsa. Kashi 65% na kuri’un Arewa ne suka cece shi, amma yau shi ne ke raina Arewar. Arewa za ta haɗe da Gabas, mu mayar da shi tekun da ya fito."
Mutane sun yi wa Ibrahim Modibbo martani

Asali: Twitter
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da jama'a suka yi wa maganganun Ibrahim Maikudi:
@HaadiJimoh:
"Ina fatan ka lissafa ka kuma fahimci cewa yankin Arewa ta Tsakiya yanzu Arewa ce, ba rabin Yarbawa ko wasu ba.
"Zai samu kuri’u masu yawa a Kogi, Kwara, Filato, babban birnin tarayya (FCT), da Neja. Hakanan, Kano, Kaduna, Katsina, Borno da wasu jihohin za su kada masa kuri’a.
"Ko da bai ci wadannan wuraren ba, bambancin ba zai kai yadda kake tunani ba. Ku shirya sosai domin abin da ke tafe ya fi girman guguwar siyasa.
"Gaisuwa ta musamman ga Daddy El-Rufai. Har yanzu ina jin zafin matakinsa na baya-bayan nan, amma abin ya shafi muradi ne kuma dole ne a kare shi."

Kara karanta wannan
'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka
@Ubaidullahkaura
"Me ya hana mu tattauna kan ɗan takarar da kullum yake faduwa zabe, dan jihar Adamawa?"
@OMOIKORODUOGA1:
"Shi dai tuni ya zama shugaban kasa. Magana ta kare."
@Mustapha_Abba_A:
"Kuma in sha Allahu za a kayar da shi."
@A_wahab_I:
"Hmmm, a wancan lokacin mutum shi kadai ne gayya, amma yanzu fa shi ne ke riƙe da mulki. Allah ya yi ikonsa a kansa."
'Mutum 1 da zai kwace mulki hannun Tinubu'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nana Kazaure, tsohuwar kakakin yakin neman zaben Obidatti a 2023, ta yi hasashen wanda zai iya lashe zaben 2027.
Ta bayyana cewa Peter Obi na da damar lallasa Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 idan majalisa ta amince da wata dokar da za ta bai wa 'yan takara damar tsayawa ba tare da jam'iyya ba.
Nana Kazaure ta ƙara da cewa Obi yana da babban damar cin zabe a 2027 idan wannan doka ta samu amincewa daga majalisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng