APC Ta Yi Bayani kan Shirin Sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

APC Ta Yi Bayani kan Shirin Sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

  • Reshen Arewa maso Tsakiya na APC na shirin kwanto wa jam’iyya da hankali gabanin zaben 2027 ta hanyar neman kujerar Kashim Shettima
  • Manyan ’yan siyasa daga jihohin Filato, Nasarawa, Binuwai, Neja, Kogi da Kwara sun koka kan yadda suke ganin an bar yankin a baya wajen shugabanci
  • Sai dai Daraktan Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce a halin yanzu, babu wani yunkuri na mataimakin shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaJam’iyyar APC mai mulki ta musanta ikirarin cewa akwai sabani tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

Haka kuma, jam’iyyar ta yi watsi da jita-jitar cewa Tinubu yana shirin sauya mataimakinsa kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Uromi: Barau ya yi alkawari bayan ziyarar iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

Kashim
Arewa ta Tsakiya na neman kujerar Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa duk da cewa Tinubu bai bayyana aniyarsa ta yin takara a karo na biyu ba, magoya bayansa da manyan jiga-jigan jam’iyyar sun riga sun fara gangamin nema masa goyon baya,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta musanta shirin musanya Kashim Shettima

Daily Post ta ruwaito daraktan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim, ya ce rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu a ba shi da tushe.

Ya ce:

“Wannan dai shaci-fadi ne kawai ba tare da wata hujja ba. Maganganu ne da ake yi a wuraren shan giya, don haka bai kamata a dauke su da muhimmanci ba.”
“Sannan ko da a ce a wani dalili Shugaban Kasa zai yi tunanin sauya mataimakin nasa, ba zai iya yanke wannan hukunci shi kadai ba. Wajibi ne ya tattauna da muhimman jiga-jigan siyasa kafin yanke irin wannan shawara.'"

APC: Arewa ta Tsakiya na neman kujerar Shettima

Kara karanta wannan

Gwamna ya ciri tuta, jam'iyyar APC Ta ba shi tikitin takara a zaɓen 2027

A gefe guda, jiga-jigan siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya sun sabunta kiran da suke yi na neman kujerar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.

An bayyana bukatar ne a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, wakilan jihohin Filato, Nasarawa, Binuwai, Neja, Kogi da Kwara karkashin jagorancin Farfesa Nghargbu K’tso.

Kashim
Mataimakin shugaban kasa, Kashi Shettima Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

A wata sanarwa da suka fitar bayan taron, sun bukaci cewa idan APC ta ba Tinubu fifiko na tsayawa takara a karo na biyu, dole ne a ba Arewa ta Tsakiya kujerar mataimakin shugaban kasa.

Farfesa Nghargbu ya ce:

“Daga cikin yankunan siyasa guda shida na Najeriya, Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas ne kadai ba su taba samun shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba cikin shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya na jamhuriyya ta hudu.”
“Lamarin Arewa ta Tsakiya ya fi muni fiye da na Kudu maso Gabas, domin a kalla yankin Kudu maso Gabas ya taba samun Dr Alex Ekwueme a matsayin mataimakin shugaban kasa daga 1979 zuwa 1983."

Kara karanta wannan

APC: Jiga-jigan PDP sun fitar da matsaya kan kawancen jam'iyyu gabanin 2027

APC: Arewa maso Tsakiya na neman daidaito

Farfesa Nghargbu K’tso ya jaddada cewa lokaci ya yi da yankin zai bukaci cikakken hadin kai daga sauran yankunan Arewa.

Ya ce:

“Wannan batu ne na adalci. Muna son a dauke mu ba kawai a matsayin ‘yan rakiyar siyasa ba, sai dai a matsayin cikakkun ‘yan kasa masu hakkin shiga harkokin mulki,."

Da yake mayar da martani kan wannan bukata, Bala Ibrahim na APC ya yi watsi da ita, yana mai cewa ba ta da tushe kuma “ta mutu tun kafin a haifeta.”

Bala Ibrahim ya ce:

“Bai kamata Arewa ta Tsakiya ta dauki shugabancin kasa ko mataimakin shugaban kasa a matsayin hakkinta ba, musamman idan aka kwatanta da yawan kuri’un da take bayarwa a zabe idan aka hada da yankin Arewa maso Yamma.”
“Sun sha yin irin wadannan bukatu a baya, amma yawanci ba su da amfani sai dai kara haifar da hayaniya mara tushe a siyasa."

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

Ya jaddada cewa bai kamata a fara maganar rabon mukaman siyasa ba, tun da Tinubu bai kammala zangon mulkinsa na farko ba.

Kashim Shettima ya bar Najeriya

A baya, kun samu labarin cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Dakar da ke Senegal domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a wani muhimmin biki.

Ziyarar Sanata Shettima tana da nasaba da bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai na ƙasar Senegal daga Turawan Faransa, wanda aka gudanar a babban birnin kasar, Dakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel