'Ba Zan Yi Sata ba': Ɗan Majalisa Ya Cire Tsoro a gaban Ƴan Mazabarsa bayan Shan Suka
- Dan majalisar wakilai a Niger, Joshua Audu Gana ya ce ba zai saci kudi don faranta wa al'ummarsa rai ba, bayan fuskantar suka a mazabarsa
- Yayin taron PDP a Mokwa, Gana ya ce wasu bukatu ba su dace ba, domin aiki a gwamnati yana da matakan da ke shafar aiwatar da ayyuka
- Ya bayyana cewa rashin isassun kudade da kuma kasancewarsa a jam'iyyar adawa na hana shi aiwatar da ayyukan da ake bukata a mazabarsa
- Maganganunsa sun jawo cece-kuce daga wasu mutanensa, yayin da mabiyansa suka ce za su duba hanyoyin gyara jagorancinsa nan gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Lavun/Mokwa/Edati a Jihar Niger, Joshua Audu Gana, ya kare kansa kan gazawarsa wajen aiwatar da ayyukan mazaba.
Hon. Gana ya tabbatar da cewa ba zai saci kudin al'umma don faranta wa al'ummarsa rai ba bayan sukar da yake sha.

Source: Instagram
An soki Audu Gana kan rashin katabus
Wannan magana ta fito ne a taron jam’iyyar PDP da aka yi a karamar hukumar Mokwa, bayan wasu shugabannin jam'iyyar sun nuna rashin gamsuwa da aikinsa, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Suleiman Kupanti, shugaban PDP na yankin, ya yi suka kan rawar da Gana ke takawa ga yan mazabarsa.
Hon. Gana ya bayyana cewa wasu daga cikin abubuwan da ake bukata daga gare shi ba su dace ba, yana mai bayanin cewa mukamin siyasa yana da tsarin gudanarwa da nauyin da ke tattare da shi.
Ya tabbatar wa da mahalarta taron cewa, ko da bai iya aiwatar da komai ba, zai mika bukatunsu zuwa hukumomin da suka dace.
Ya ce:
"Ina gode wa Allah cewa ba ni ne Allah ba, ku duba kasafin kudi na kasa da rabon da aka ba mazabar mu. Sai an ware kudade yadda ya kamata sannan za ku iya tuhumata."

Source: Facebook
Hon. Gana ya fadi gaskiya kan kasafin kudi
Dangane da zargin cewa bai yi ayyuka ba saboda rashin kudade, Gana ya ce kasancewarsa a jam’iyyar adawa na iya hana shi samun kudaden da ya dace.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa APC mai mulki ce ke rike da mafi yawan kasafin kudi, Daily Post ta ruwaito.
Ya kwatanta halin da yake ciki da na lokacin da PDP ke mulki, yana mai cewa tsarin siyasa na yanzu ya sha bamban da na baya.
Duk da haka, maganganunsa sun haddasa cece-kuce a tsakanin al'ummarsa, inda wasu suka nuna takaici tare da bukatar ganin ayyuka ba wai bayanai kawai ba.
Duk da wannan rikici, magoya bayan Gana sun bayyana kudirinsu na koya daga wannan matsala domin inganta jagorancinsa a nan gaba.
Legit Hausa ta zanta da wani a yankin
Wani a yankin Lavun/Mokwa/Edati da ke jihar Niger ya koka kan jagorancin ɗan majalisar.

Kara karanta wannan
"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi
Nura Saleh ya za a iya cewa akwai matsala ganin yadda yake salon jagorancinsa a yankin.
"Sai dai ina yi masa uzuri saboda yadda yanayin kasar take, za ka samu yafi da yawa daga takwarorinsa kokari."
- Cewar Nura
Ya shawarci dan majalisar ya dauki hakan a matsayin kalubale tun da har manyan jam'iyyar sun koka.
Kotu ta tabbatar da nasarar Audu Gana
A baya, kun ji cewa Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Joshua Audu Gana na jam’iyyar PDP a mazabar Lavun/Mokwa/Edati a Niger.
Kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe da ta yi a ranar 11 ga watan Satumbar 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

