'Magagin Fadi Zabe Bai Sake Shi ba,' Fadar Shugaban Kasa Ta Tankawa Peter Obi

'Magagin Fadi Zabe Bai Sake Shi ba,' Fadar Shugaban Kasa Ta Tankawa Peter Obi

  • Mai ba da shawara ga Bola Ahmed Tinubu kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya caccaki tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi
  • Bwala ya zazzage Mista Obi ne saboda kalaman da tsohon ɗan takarar ya yi game da shugaban kasa kan yadda yake gudanar da Najeriya
  • Obi ya ce Tinubu yana cika alkawarin da ya dauka, domin farashin abubuwa sun tashi, yana ci gaba daga inda Muhammadu Buhari ya tsaya
  • Kalaman ba su yi wa Bwala dadi ba, ya bayyana cewa Obi yana yin kalaman ne saboda zafin faduwa a zaɓen 2023, wanda Tinubu ya yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaDaniel Bwala, mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa, ya ce Peter Obi bai warke daga gigin rashin nasara da ya yi masa a zaɓen shugaban kasa na 2023 ba.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

Peter Obi, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, ya yi ya yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shagube a kan yadda ya ke gudanar da jagorancin Najeriya.

Tinubu
An soki Obi kan caccakar Tinubu Hoto: Peter Obi/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi ikirarin cewa Tinubu yana cika alkawuran kamfen da ya yi, kuma ya dora a kan aikin da Muhammadu Buhari ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi ya ce Tinubu yana aikata abubuwan da ya yi alkawari ga al'umma, ganin yadda ake samun karin tsadar rayuwa, wanda ya zama kari a kan abin da Buhari ya yi.

Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Obi

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, Bwala ya Peter Obi da zuba karairayi, yana mai cewa Najeriya ta guje wa haɗari da ba ta zaɓi Obi a matsayin shugaban kasa ba.

Ya ce:

“Yayin da nake sauraron Peter Obi, yana ƙoƙarin yin adawa da gwamnati, ya na magana ne cike da rashin gaskiya.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi barazanar da ya yi wa Wike kan rasa mukaminsa, ya ba shi mamaki

Shugaban kasa ta caccaki Peter Obi

Daniel Bwala ya ci gaba da caccakar Peter Obi, inda ya ce bai warke daga shan kaye a hannun APC ba yayin zaben shekarar 2023.

Peter
Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Ya kara da cewa yana mamakin halin da Peter Obi ya ke ciki a yanzu, ganin cewa yana fafutuka ne na neman yadda za a sake ba shi dama ya nemi kujerar shugaban kasa a 2027.

'Duk a yaye an rabu da shi ya a duniyarsa, yana kokarin yadda zai shawo kan magoya bayansa game da ba shi dama karo na biyu don sake fito wa takara a zaben 2027.'

'Dalili na na shukar shugaban kasa,' Bwala

A wani labarin, mun wallafa cewa Daniel Bwala ya bayyana dalilin da ya sa ya rika adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a lokacin da ya ke cikin jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya bayyana cewa daya daga cikin ayyukan jam’iyyar adawa shine su caccaki gwamnati mai mulki da kuma daukar nauyin aikinta, ba wai don ya ki jinin gwamnatin Bola Tinubu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng