Jiga Jigan PDP Sun Fitar da Matsaya kan Kawancen Jam'iyyu gabanin 2027

Jiga Jigan PDP Sun Fitar da Matsaya kan Kawancen Jam'iyyu gabanin 2027

  • Wasu daga cikin manyan shugabannin PDP sun ce za su hada kai da jam’iyyun adawa don kifar da gwamnatin APC da Bola Tinubu ke jagoranta
  • Jagoran tafiyar a Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce sun fara tattaunawa da NNPP, PRP da wasu ‘yan APC kan yadda za a cimma wannan manufa
  • Ya kara da bayyana cewa wasu manyan ‘ya’yan APC da ke rike da muƙamai a jihar Katsina da gwamnatin tarayya suna shiga tafiyar
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa ana son a hada kai da tafiyar tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, don korar Tinubu daga ofis

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina –Jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Katsina sun bayyana shirin su na shiga sabuwar hadakar jam’iyyun adawa da aka kafa domin kwace mulki daga hannun APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo

Shugabannin PDP na jihar, ƙarƙashin jagorancin Dr. Mustapha Inuwa, sun bayyana shirin shiga wannan hadaka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Katsina.

Atiku
Ana shirin kara wa hadakar Atiku kwari Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar This Day ta bayyana cewa Inuwa, wanda tsohon Sakataren gwamnatin Katsina ne, ya bayyana wa mahalarta taron cewa tattaunawa ta yi nisa kan yadda za a samar da hadaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa ana faftukar tabbatar da hadaka mai karfi domin kifar da APC a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

PDP za ta haɗa kai wajen fatattakar APC

Duk da cewa Inuwa bai ambaci cewa za su shiga hadakar Atiku kai tsaye ba, wata majiya mai ƙarfi daga cikin jam’iyyar ta shaida wa jaridar cewa sun cimma matsaya kan bin sabon tafarkin Atiku Abubakar.

Atiku
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Mun fara tattaunawa da 'yan NNPP, PRP da kuma wasu manyan jiga-jigan APC domin kafa hadaka ta siyasa don zaɓen 2027.”

Kara karanta wannan

Yadda 'yan siyasar Najeriya ke rububin sauya jam'iyya gabanin zaben 2027

“Wataƙila zai ba ku mamaki ku ji cewa wasu daga cikin ‘ya’yan APC da ke mara wa wannan tafiya baya suna rike da muƙamai masu muhimmanci a gwamnati, a matakin jiha da na tarayya.”

2027: Wadanda ke neman fatattakar APC

Mustapha Inuwa ya bayyana cewa 'yan sabuwar tafiyar ‘yan adawa, waɗanda suka haɗa da manyan ‘yan siyasa daga Katsina da wajen jihar za su dunkule waje guda don zabe mai zuwa.

A taron da aka gudanar a Kaduna, manyan ‘yan siyasar PDP da suka zauna kan nemo mafita sun hada da tsohon Sakataren PDP na Ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri.

Sauran sun hada da tsohon Sanata mai wakiltar yankin Daura, Ahmed Babba Kaita da kuma Ahmed Musa Yar’adua.

'Mu tallata APC,' Gwamnan Imo

A baya, kun samu labarin yadda shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bukaci takwarorinsa da su tashi tsaye wajen tallata APC.

Ya fadi haka ne a wan taro da ya gudana a Abuja, wanda a nan ne shugabannin jam’iyyar suka tattauna batutuwan da ke gaban APC kafin babban zaɓen kasa mai zuwa da shirin 'yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel