Zaben 2027: Gwamnan Nasarawa Ya Zabi Wanda Zai Gaje Shi? Ya Fadi Gaskiya

Zaben 2027: Gwamnan Nasarawa Ya Zabi Wanda Zai Gaje Shi? Ya Fadi Gaskiya

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya fito ya yi magana kan batun cewa ya zaɓi wanda zai gaje shi a shekarar 2027
  • Malam Abdullahi Sule ya musanta cewa ya zaɓi wani ɗan takara da zai gaje shi idan ya kammala wa'adinsa karo na biyu
  • Ya buƙaci mutanen jihar da su yi watsi da jita-jitar, ya ce zai ci gaba da ayyukan raya ƙasa kafin ya bar kan kujerar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya zaɓi wanda zai gaje shi a zaɓen 2027.

Gwamna Abdullahi Sule ya ƙaryata iƙirarin da wasu ƴan siyasa ke yi kan cewa ya zaɓe su a matsayin ƴan takarar da ya fi so su gaje shi a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Matawalle ya tabo batun dokar ta baci a Zamfara, ya ba Tinubu shawara

Gwamna Sule ya musanta zabar magaji
Gwamna Abdullahi Sule ya musanta zabar wanda zai gaje shi Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin Jama’a, Kwamared Peter Ahemba, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na kowane wata da ya gudanar a ranar Laraba a birnin Lafia, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Nasarawa ya musanta jita-jitar magaji

Gwamna Sule ya buƙaci jama’a da magoya bayansa su yi watsi da jita-jitar, yana mai cewa wasu ƴan siyasa ne ke yaɗa ta da nufin amfani da sunansa don cimma muradun siyasa.

Peter Ahemba ya bayyana jita-jitar a matsayin abin yaudara da karkatar da hankalin jama’a, inda ya zargi wasu ƴan siyasa da ƙoƙarin yaudarar al’umma.

"Muna son bayyanawa a fili cewa Gwamna Abdullahi Sule bai zaɓi wani ɗan takara da zai gaje shi a shekarar 2027 ba."
"Duk wani wanda aka ba muƙami da ke goyon bayan irin wannan iƙirari yana nuna rashin biyayya, kuma gwamna ba zai lamunci irin hakan ba daga yanzu."

- Kwamared Peter Ahemba

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure a sakatariyar APC, matasa su kusa lakaɗawa ciyaman duka

Yaushe gwamna zai zaɓi magajinsa?

Ya buƙaci jama’a su yi watsi da duk wani ɗan siyasa da ke iƙirarin cewa gwamnati ta zaɓe shi a matsayin ɗan takarar gwamna na 2027.

“A lokacin da ya dace, mutanen Nasarawa za su yanke shawarar wanda suke so ya zama gwamna a shekarar 2027."
"Gwamna Sule har yanzu ya na da sama da shekaru biyu domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa ga al’umma, me ya sa ake neman karkatar da hankalinsa?"

- Kwamared Peter Ahemba

Gwamna Sule na Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Gwamna Abdullahi Sule ya tabbatarwa magoya bayansa da al’ummar jihar cewa zai ci gaba mai da hankali kan shugabanci, kuma ba zai bari wasu su ɗauke masa hankali ba.

Ya bukaci jama’a su kasance masu bin doka da oda tare da sa ran samun ƙarin ayyukan ci gaba a cikin shekaru biyu da suka rage na wa’adinsa.

Gwamna Sule ya naɗa sababbin kwamishinoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa bayan ya yi sallama.

Gwamna Abdullahi Sule ya naɗa sababbin kwamishinoni guda 16 tare da miƙa sunayensu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng