INEC Ta Aika Sako ga Sanata Natasha kan Shirin Koro Ta daga Majalisar Dattawa

INEC Ta Aika Sako ga Sanata Natasha kan Shirin Koro Ta daga Majalisar Dattawa

  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta karɓi cikakkun bayanan masu ƙorafin da ke neman yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye
  • Sanatar, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na fuskantar matsin lamba tun da ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da neman ta
  • INEC ta bayyana cewa ta riga ta sanar da Natasha cewa wasu cikin mutanen da take wakilta sun aika da buƙatarsu na neman raba ta da ofis

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaHukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya game da yunkurin yi mata kiranye.

Hukumar INEC ta ce ta kuma karɓi cikakkun bayanan masu ƙorafin waɗanda ba su cika takardun da suka shigar a baya da kyau ba.

Kara karanta wannan

Natasha: INEC ta gano kuskure a kokarin yi wa Sanata kiranye, ta fadi matakin gaba

Natasha
INEC ta tura sakon shirin kiranye ga Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa wannan sanarwa ta yi daidai da tanadin sashe na 2 (a) na dokokin hukumar kan kiranye na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka isar da sakon tsige Sanata Natasha

A wata sanarwa da Ruth Oriaran Anthony, sakatariyar hukumar INEC ta sanya wa hannu, ta ce an tabbatar da cewa an isar da sakon kiranyen Sanata Natasha gare ta.

Sanarwar ta ce:

"A bisa tanadin sashe na 69 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, da aka yi wa gyara, na rubuto don sanar da ke cewa mun karɓi ƙorafi daga wakilan masu zaɓe da aka yi wa rajista a mazaɓarki, waɗanda ke neman a tsige ki daga majalisar dattawa."
"Wannan takarda an aika ta ga shugaban majalisar dattawa kuma an wallafa ta a shafin yanar gizon hukumar. Mun gode."

Yadda aka gyara bukatar kiranyen Natasha

Kara karanta wannan

Abin da Hukumar INEC ta yi kan shirin yi wa Natasha kiranye daga Majalisa

A wata sanarwa da INEC ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa yanzu ta karɓi sababbin bayanan tuntuɓa daga wakilan masu ƙorafin da ke neman a tsige Sanata Natasha.

Sam Olumekun, kwamishina na ƙasa a INEC kuma shugaban sashen bayani da wayar da kan masu zaɓe, ya bayyana cewa an isar da wasiƙar sanar da Sanata Natasha zuwa wurin aikinta.

Natasha
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Twitter

Ya ce:

"Mataki na gaba shi ne tantance jerin sunayen waɗanda suka sa hannu a ƙorafin, don tabbatar da cewa sun fi rabin (50%) na masu zaɓe da aka yi wa rajista a mazaɓar. Za a yi wannan aikin a kwanaki masu zuwa."
"Sakamakon tantancewar da za a yi, wanda za a wallafa a bainar jama’a, zai nuna matakin da hukumar za ta ɗauka na gaba. Muna kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da dukkanin dukkanin matakan kiranyen a bainar jama'a."

An yi hukuncin karshe kan korafin Natasha

Kara karanta wannan

Daga karshe Sanata Natasha ta nemi afuwar majalisar dattawa? Ta fito ta fede gaskiya

A wani labarin, mun wallafa cewa kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya yanke shawarar watsi da zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar gabanta.

Sanata Natasha, ta bayyana cewa shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya sha nemanta da lalata a lokuta daban daban, wanda hakan ya sa ya ke tsangwamarta a zauren majalisa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel