Jerin na Kusa da Buhari da Jiga Jigai da Ake Zargin Za Su Bar APC zuwa SDP

Jerin na Kusa da Buhari da Jiga Jigai da Ake Zargin Za Su Bar APC zuwa SDP

  • APC na fuskantar barazanar ficewar manyan 'ya'yanta, musamman masu biyayya ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin zaɓen 2027
  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar SDP saboda rashin daidaito tsakanin manufofin APC da ra'ayinsa
  • Ana zargin wasu shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC kamar Abubakar Malami SAN suna shirin barin APC saboda rashin gamsuwa da shugabancinta
  • Shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC sun nuna rashin jin daɗi da shugabancin APC na yanzu, wanda ya sa suke tunanin sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tun bayan ficewar Nasir El-Rufai zuwa SDP, jam'iyyar APC na ci gaba da fuskantar barazana.

El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu biyayya ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa akwai rashin daidaito tsakanin sabon shugabancin APC da ra'ayinsa, wanda ya sa ya bar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

Ana zargin na kusa da Buhari ka iya barin APC zuwa SDP
Wasu na kusa da Buhari da ake zargin za su bar APC zuwa SDP. Hoto: @elrufai, @officialABAT, @MBuhari.
Asali: Twitter

Ana zargin 'yan APC za su koma SDP

Punch ta ce El-Rufai ba shi kaɗai ba ne daga cikin shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC da ke shirin barin APC duba da yadda suke kushe salon mulkin Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CPC ita ce jam'iyyar da Buhari ya jagoranta kafin haɗewar da aka yi don kafa APC a 2014 wanda ya yi sanadin kifar da gwamnatin Goodluck Jonathan karkashin jam'iyyar PDP.

Wasu daga cikin shugabannin CPC da ke shirin barin APC sun haɗa da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami SAN.

Jiga-jigan jam'iyyar sun nuna rashin gamsuwa da shugabancin jam'iyyar da ake tafiyarwa a yanzu wanda aka bar mafi yawan wadanda suka ba da gudunmawa a gefe.

Legit Hausa ta duba muku jerin wadanda ake zargin suna yunkurin komawa APC zuwa SDP saboda yanayin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

1. Ahmed Lawan

Sanata Ahmed Lawan, wanda ke cikin majalisar dattawa tun 1999, yana daga cikin wadanda ake zargin sun shirya barin APC zuwa SDP.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Sai dai tsohon shugaban majalisar ya musanta shirin shiga SDP domin tarewa da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai.

Ahmed Lawan ya yi magana kan barin APC zuwa SDP
Sanata Ahmed Lawan ya musanta labarin zai bar APC zuwa SDP. Hoto: Aswiaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

2. Abubakar Malami

Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami shi ma ana zargin yana shirin barin APC saboda yadda take gudanar da shugabanci.

Malami ya rike mukamin antoni janar na tarayya a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma ya kasance na hannun damansa.

3. Abdullahi Adamu

Abdullahi Adamu wanda tsohon gwamna ne a jihar Nasarawa, ya na cikin masu biyayya ga Buhari da ake zargin za su fice daga APC.

Tsohon shugaban APC, ya kasance tsohon sanata kafin sauya shugabanci daga gwamnatin Buhari zuwa na Bola Tinubu.

Bayan Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, sai ya yi murabus daga kujerar shugaban APC, tun daga lokacin aka daina jin duriyarsa.

4. Rotimi Amaechi

Tsohon gwamnan Rivers na daga cikin wadanda ake zargin sun shirya haɗaka domin barin APC da suka dade a cikinta.

Kara karanta wannan

El Rufai ya fara karɓe magoya bayan Kwankwaso, jiga jigan NNPP sun koma SDP

Amaechi yana daga cikin manyan APC da suka gana a makon jiya a Abuja tare da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai da sauran yan adawa.

Tsofaffin ministocin Buhari da ake zargin za su bar APC
Rotimi Amaechi na daga cikin wadanda suna gana da ƴan adawa a Abuja. Hoto: Hon. Rotimi Chibueke Amaechi.
Asali: Facebook

5. Kayode Fayemi

Kayode Fayemi, minista a mulkin Muhammadu Buhari shi ma ya nuna damuwa game da salon shugabancin Bola Tinubu da APC.

Tsohon gwamnan Ekiti na daga cikin jiga-jigan APC wadanda suka ba da gudunmawa wurin kafa gwamnatin Bola Tinubu.

5. Babachir Lawal

Tsohon sakataren Gwamnatin Tarayya a mulkin Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka soki tikitin Musulmi da Musulmi, cewar Vanguard.

Babachir Lawal na daga cikin wadanda suka halarci taro da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai kan dokar ta-ɓaci a Rivers da kuma tattaunawa kan zaben 2027.

Buhari ya dakatar da shi daga muƙaminsa na sakataren gwamnati a 2017 saboda zargin almundahana da cin hanci da rashawa inda aka maye gurbinsa da Boss Mustapha, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP

Jiga-jigan APC sun gana da yan adawa a Abuja
Babachir Lawal da sauran yan APC sun yi zama da Atiku da El-Rufai a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: UGC

Matsalolin da ke cikin shirin haɗaka a 2027

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon kusa a APC, Salihu Lukman ya tabbatar da cewa ana tattaunawa kan hadakar jam’iyyun adawa don fuskantar Bola Tinubu a 2027.

'Dan siyasar ya musanta cewa an kammala tattaunawar, ya na mai cewa ana ci gaba da tsara tsarin hadakar jam'iyyun hamayya duk da matsalolin da ke ciki.

Lukman ya ce ya bayyana muhimman abubuwa biyu da aka fi ba karfi domin tabbatar da tsara tafiyar ba tare da samun tasgaro daga yan siyasa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng