Shirin Fatattakar Tinubu Ya Samu Cikas bayan Matsayar Sakataren PDP kan Haɗakar Atiku

Shirin Fatattakar Tinubu Ya Samu Cikas bayan Matsayar Sakataren PDP kan Haɗakar Atiku

  • Da alama tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP zai fara fuskantar ƙalubale kan shiga haɗakar adawa da Bola Tinubu
  • Atiku, tare da haɗin gwiwar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da Peter Obi, sun sanar da jagorantar ƙawancen jam'iyyu
  • Sai dai Sakataren PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda kotu ta mayar wa da muƙaminsa, ya ba su, ba batun haɗaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT ABUJASakataren PDP da kotu ta mayar mukaminsa kuma aminin Nyesom Wike, Sanata Samuel Anyanwu, ya ce an kawo ƙarshen rikicin cikin gida a jam'iyyar. Ya shawarci ƴaƴan PDP da ke tattaunawar haɗakar jam’iyyu don zaɓen 2027 da su sake tunani tare da haɗa kai wajen gina PDP domin ƙarfafa ta.

Kara karanta wannan

"Da gaske ake haɗakar lallasa gwamnatin Tinubu a 2027," Tsohon ɗan takara

Atiku
PDP ta nemi haɗa kan ƴaƴanta Hoto: Sen Samuel Nnaeneka Anyawu/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wata hira ta keɓanta ga jaridar Punch, Anyawu ya yi kira ga ƴan PDP da su mayar da hankali kan ƙarfafa jam’iyyar a maimakon fafutukar kafa wata haɗaka. Kiran da Anyanwu ya yi na zuwa ne bayan sanarwar da Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Nasir El-Rufa'i na SDP suka yi ma kafa haɗakar kifar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

PDP ba ta san da shirin haɗakar Atiku ba

Anyanwu, wanda ya ce bai san da wannan haɗakar da su Atiku ke jagoranta ba, ya bukaci yanzu lokaci ne da ƴan PDP za su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jaddada cewa PDP ba ta cikin kowace irin haɗaka, yana mai rokon waɗanda ke neman kawar da Shugaba Tinubu ta hanyar haɗakar jam’iyyu da su shigo PDP.

Ya ce:

"PDP ba ta cikin kowace haɗaka; ba a gayyace mu zuwa kowace tattaunawa ba. A zahiri, ba mu taɓa yin wata tattaunawa kan haɗaka ba. PDP tana da ƙarfi a matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi da jihohi.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

A ganina, waɗanda ke magana kan haɗaka su shigo PDP. Rikicin ya ƙare, don haka mutane su shigo PDP maimakon PDP ta shiga kowace haɗaka."

PDP: Anyanwu ya yi maraba da komawa mukaminsa

Da yake magana kan hukuncin kotu da ya maido shi kan mukaminsa, Sanata Anyanwu ya bayyana jin daɗinsa, ya na mai cewa hukuncin Kotun Koli ya kawo ƙarshen rikici jam’iyyar.

Atiku
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Sanata Anyanwu ya ce:

"Kotun Koli ita ce babbar kotu, kuma ni ne Sakataren Ƙasa na PDP. Ban riƙe kowa a rai ba. Lokaci ƙalilan ne ya rage, don haka abin da muke buƙata shi ne haɗa kai don sake inganta jam’iyya." "Ko da yake na sha wuya kuma na fuskanci matsi, amma na jure duka. Yanzu lokaci ne da za mu haɗa kai domin farfaɗo da PDP.
Haka kuma akwai buƙatar gaggauta kiran taron kwamitin zartarwa domin mu zauna mu fuskanci juna, mu fadi gaskiya, kuma mu nemi gafara idan akwai bukatar haka."

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Kotu ta yi hukunci kan kujerar Sakataren PDP

A baya, mun wallafa cewa Kotun ƙoli ta bayyana Sanata Samuel Anyanwu, wanda makusancin Nyesom Wike ne, a matsayin halastaccen Sakataren jam’iyyar PDP.

Sanata Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun shafe lokaci suna gwabza rikici kan wannan matsayi, lamarin da ya haddasa rabuwar kai a tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng