"Da Gaske ake Haɗakar Lallasa Gwamnatin Tinubu a 2027," Tsohon Ɗan Takara
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Pat Utomi, ya ce ana gina haɗakar jam’iyyu da ƴan siyasa don kayar da Bola Ahmed Tinubu
- Ya faɗi haka ne bayan bayyanar haɗakar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da Peter Obi domin ragargazar gwamnatin APC a 2027
- Utomi ya ce manyan ƴan siyasa daga APC da PDP sun nuna sha’awar shiga sabuwar haɗakar siyasa, a ceto ƴan ƙasa daga wahala
- Ya kuma bayyana yadda ake shirin zaɓo jam'iyyar da za a yi amfani da ita wajen fafata wa da gwamnatin Tinubu a filin zabe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Farfesa Pat Utomi, ya bayyana matakan da ake ɗauka don ƙirƙiro haɗakar jam’iyyu da ƙungiyoyi gabanin 2027

Kara karanta wannan
Akwai matsala: SDP na kokarin kawo cikas ga shirin El Rufai na yin hadaka da 'yan adawa
Farfesa Utomi ya bayyana cewa babbar haɗakar za ta kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027, yana mai cewa wannan aiki ne mai muhimmanci don ceto Najeriya.

Asali: Twitter
A wata hira da ta keɓanta ga Punch News, Utomi, wanda ke cikin manyan jagororin ƙungiyoyin adawa, ya ce za a haɗa kai da ƴan siyasa daga jam’iyyun APC da PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa tuni wasu ƙusoshin jam'iyyun suka nuna sha’awar shiga wannan haɗaka, baya ga sauran wasu jam’iyyu guda biyar.
Ƴan siyasa na son kawar da gwamnatin Tinubu
Fitaccen masanin tattalin arziki, Farfesa Pat Utomi, ya ce tuni manyan jam’iyyun adawa da ƙungiyoyi daban-daban suka fara nazarin wacce jam’iyya ce za ta zama babban dandali na zaɓen 2027.
Utomi ya ce:
"Wannan aiki ne mai girma. Najeriya na cikin mawuyacin hali a daidai lokacin da tsarin duniya ke sauyawa."
Ya ci gaba da bayyana cewa sabuwar dabarar da suke amfani da ita ita ce tattaunawa da manyan jagorori masu tasiri a cikin jam’iyyun APC da PDP.
Ana rainon SDP don nasara kan Tinubu
Utomi ya kuma bayyana cewa jam’iyyar SDP tana cikin jerin jam’iyyun da ake aiki da su domin kafa wannan haɗakar siyasa, tare da wasu jam’iyyu guda biyar da ake ci gaba da nazari a kansu.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Jama’a da dama na shirin ficewa daga APC da PDP, kuma suna tuntuɓar mu. Amma dole ne mu tabbatar da cewa ginshikin wannan haɗaka ya kafu sosai."
Da aka tambaye shi yadda za a daidaita buƙatun ƙungiyoyin siyasa daban-daban da ke son shiga haɗakar, Utomi ya ce abin da ke jagorantar su shi ne sadaukarwa.
Haka kuma ya ce masu shiga haɗakar na son a gina tsarin shugabanci mai ɗorewa wanda za a yanke shawara tare a kan muhimman batutuwa.
Tinubu: Jiga-jigan ƴan siyasa sun haɗe kai
A baya, mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya tabbatar da kafa wata babbar haɗaka ke ƴan adawa.
Ya bayyana cewa an samar da haɗakar ne domin ƙalubalantar jam’iyyar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027 da haɗin gwiwar sauran ƴan adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng