"Tinubu Ya Saba da Tsarin Jari Hujja," NNPP Ta Haramta Dokar Ta Ɓacin Ribas

"Tinubu Ya Saba da Tsarin Jari Hujja," NNPP Ta Haramta Dokar Ta Ɓacin Ribas

  • Jam'iyyar hamayya ta NNPP ta zargi Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da wuce makaɗi da rawa kan dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce rikicin siyasar Jihar Ribas bai kai matakin da za a ayyana dokar ta-ɓaci ba
  • A tattaunawarsa da Legit, Shugaban NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi zargin cewa Tinubu ya saba da mulkin jari-hujja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaJam’iyyar hamayya ta NNPP ta soki matakin Shugaba Bola Tinubu na kakaba dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni. A ranar Talata ne Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar bayan rikicin siyasa da ya ɗauki lokaci yana ci gaba tsakanin majalisar jiha masu goyon bayan Nyesom Wike da gwamna.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Ladipo
NNPP ta soki dokar ta ɓaci a Ribas Hoto: Ladipo Johnson/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida. Bayan daukar matakin ne kuma, sai Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan rundunar sojan ruwa, Ibok-Ete Ibas (ritaya), domin ya kula da harkokin jihar.

NNPP ta zargi Bola Tinubu da karya doka

A martaninta kan lamarin, jam’iyyar NNPP ta bakin mai magana da yawunta, Ladipo Johnson, ta bayyana matakin Tinubu a matsayin wanda ya ci karo da kundin tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta bayyana shi da cewa dakatar da gwamnatin, shawarace mara kan gado kuma mai matuƙar haɗari ga dimokuraɗiyya. NNPP ta ce rikicin siyasar da ke Ribas bai kai matakin da za a ayyana dokar ta-ɓaci ba, domin akwai hanyoyin da suka fi dacewa da za a iya bi don warware matsalar.

A cikin sanarwar, jam’iyyar ta ce:

"Tabbas, amfani da ikon Shugaban ƙasa don ayyana dokar ta-ɓaci bisa Sashe na 305 na Kundin tsarin mulkin 1999 ba daidai ba ne a wannan yanayi, musamman idan aka yi la’akari da sharuɗɗan da ke tattare da hakan da kuma tasirinsa ga dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Ribas: Tambuwal ya tona yadda aka yi watsi da doka a majalisa don biyan buƙatar Tinubu

NNPP ta zargi Tinubu da mulkin kama karya

Shugaban NNPP a Kano, Dakta Hashimu Dungurawa, ya zargi Bola Tinubu da aikata ba daidai ba tare da yin watsi da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Hashim
Hashimu Dungurawa, shugaban NNPP na Kano Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Asali: Facebook

A wata hira da Legit, Dungurawa ya ce:

"Shi kansa dokar ta-ɓaci, idan za a yi, akwai matakan da ya kamata a bi, akwai hukumomin da ya kamata a sanar da su da kuma sahalewa kafin a aiwatar da ita"
"Amma Tinubu ya saba da tsarin kama karya, ya saba tsari na jari hujja, tsari na son zuciya, tsari na keta alfarmar dan Adam da keta alfarmar dimokuraɗiyyar."

Dungurawa ya ce Tinubu ne Shugaban ƙasa na farko da ya cire tallafin man fetur ba tare da amincewar Majalisa ba.

Ya ce:

"Ya yanke hukunci ba tare da tuntubar Majalisar Zartarwa ko Majalisar Ƙasa ba. Ya cire tallafin man fetur haka kawai, kamar Najeriya a gidansu aka haifeta."

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

APC ta yi wa gwamnatin NNPP barazana

A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar APC ta fara barazanar cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta iya sanya dokar ta ɓaci a Kano saboda kalaman tunzirin wasu jami'ai.

Barazanar ta biyo bayan kalaman mataimakin gwamnan jihar, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo na zargin matar shugaban APC, Hafsat Abdullahi Ganduje da yafutar kuɗin ƴan fansho.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng