‘Abubuwa 2 da Jam’iyyun Adawa Suka Fi Ba Karfi domin Kifar da Tinubu a 2027’

‘Abubuwa 2 da Jam’iyyun Adawa Suka Fi Ba Karfi domin Kifar da Tinubu a 2027’

  • Tsohon jigon APC, Salihu Lukman ya ce ana tattaunawa kan hadakar jam’iyyun adawa don fuskantar Bola Tinubu a 2027.
  • 'Dan siyasar ya musanta cewa an kammala tattaunawar, ya na mai cewa ana ci gaba da tsara tsarin hadakar hamayya
  • Lukman ya ce hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta hana rajistar sababbin jam’iyyu wanda yake tauye damarsu a zaɓe
  • Ya ce akwai maganar hadaka da watsar da son kai a tsakani da kuma wacce jam'iyya za a yi takara domin fuskantar Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa.

Tsohon kusa a jam'iyya mai mulki ya ce ana tattaunawa kan kafa hadaka domin fuskantar APC da Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fadi hanya 1 da jam'iyyun adawa za su ba Tinubu wahala a 2027

Halin da ake ciki kan tattaunawar jam'iyyun adawa domin fuskantar Tinubu
Tsohon kusa a APC, Salihu Lukman ya fadi matakin da ake kan hadakar jam'iyyun adawa. Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai.
Asali: UGC

Musabbin shirin hadaka kan zaben 2027

Lukman ya mayar da martani ne kan kalaman Atiku Abubakar, wanda ya ce an kammala hadakar da wasu jagororin adawa, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyun adawa sun ce manufarsu ita ce kawar da APC da Tinubu daga mulki a 2027, amma Lukman ya ce tattaunawar bata kammala ba.

A cewar Lukman:

“Dole ne a fahimta cewa har yanzu ana tattaunawa, kuma ba a kammala ba, za a sanar da mutane idan an yanke shawara.”

Ya ce wasu rahotanni na cewa akwai matsaloli a hadakar saboda rashin jituwa kan jam’iyyar da za a yi amfani da ita.

Lukman ya ce an cimma matsaya cewa za a tantance tsarin zaɓen ‘yan takara ne bayan an amince da jam’iyyar.

Ya ce idan an kammala tattaunawa, za a sanar da ‘yan Najeriya cikakken bayani tare da fara shirye-shiryen 2027.

Kara karanta wannan

2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura

Ya kara da cewa akwai ci gaba sosai a shawarwarin hadaka, kuma ana kokarin sa kowa ya yi aiki tare ba tare da son zuciya ba.

A cewarsa:

“Babban batu shi ne wacce jam’iyya za ta zama dandali na shiga zaɓe, kuma ana ci gaba da tattauna hakan.”
Shirin hadaka na ci gaba da samun karfi domin kifar da Tinubu
Salihu Lukman ya bayyana shirin jam'iyyun adawa kan tumbukr Tinubu a 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu, Peter Obi.
Asali: Facebook

Matsalolin da hadakar ke fuskanta a yanzu

Lukman ya ce akwai matsaloli kan batun rabon mukamai, amma ba a kai ga tattaunawa kan hakan a hukumance ba tukuna.

Tsohon kusa a APC ya ce batun zaɓar jam’iyya ne mafi wahala, kuma an jima ana tattauna hakan fiye da shekara guda.

Ya kuma zargi hukumar INEC da hana rajistar sababbin jam’iyyu, yana mai cewa hakan na tauye damarsu, TheCable ta ruwaito.

Salihu Lukman ya ce wasu daga cikin wadannan jam’iyyun na fuskantar rikice-rikicen da ka iya hana su shiga zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Daga bisani ya ce ana kokarin hana kowace jam’iyya da ba APC ba damar tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

Yadda aka fara samun matsala kan hadaka

Mun ba ku labarin cewa yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin fuskantar Bola Tinubu a 2027 na fuskantar cikas.

An ce hakan bai rasa nasaba da takarar Atiku Abubakar da batun karba-karba a mulki wanda Peter Obi ke goyon baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng