Zargin Lalata: INEC Ta Karbi Bukatar Yi wa Sanata Natasha Kiranye daga Majalisa

Zargin Lalata: INEC Ta Karbi Bukatar Yi wa Sanata Natasha Kiranye daga Majalisa

  • INEC ta karɓi ƙorafin da ke neman tunbuke Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa bisa dalilai na rashin gamsuwa da aikinta
  • Masu ƙorafin sun kafa hujja da sashe na 69 na kundin tsarin mulki, suna zargin sanatar da cin amanar al’ummarta da rage martabar majalisar
  • Har yanzu, INEC ba ta fitar da sanarwa ba, kuma Sanata Akpoti-Uduaghan ba ta yi martani kan ƙorafin ba, yayin da ake jiran matakin doka na gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta karɓi bukatar da ke neman yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye daga majalisar dattawan Najeriya.

Sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta karɓi ƙorafin a ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025.

'Yan mazabar Kogi ta Tsakiya sun shigar da korafin yi wa Sanata Natasha kiranye daga majalisa.
INEC ta karbi korafi daga 'yan mazabar Kogi ta Tsakiya na neman yiwa Sanata Natasha kiranye. Hoto: Natasha I Akpoti
Asali: Facebook

INEC ta karbi korafin tunbuke Sanata Natasha

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

Jaridar Punch ta rahoto cewa takardar korafin da aka shigar na dauke da taken: Korafin mazaba don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye saboda rashin gamsuwa da aikinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙorafin da aka aikawa shugaban INEC, masu ƙorafin sun bayyana wa hukumar haƙƙinsu a ƙarƙashin doka da ya ba su 'yancin neman tunbuke Sanata Natasha.

Masu ƙorafin sun ce:

“Mu da mu ka sa hannu a wannan ƙorafi, mu na da cikakkiyar rajista a matsayin masu zaɓe a mazabar Sanatan Kogi ta Tsakiya.
"Muna amfani da haƙƙinmu a ƙarƙashin dokokin Tarayyar Najeriya don neman yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye daga majalisar dattawa ta Najeriya.”

An kafa hujjar doka wajen yi wa Natasha kiranye

Masu ƙorafin sun kafa hujja da sashe na 69 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), tare da ƙa’idojin INEC na yi wa sanatar kiranye.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Sun tunatar da cewa:

"Natasha Akpoti-Uduaghan ta samu nasarar zama Sanata ne bayan shari’ar da ta kai kotun ɗaukaka ƙara, wadda a ranar 31 ga Oktoba, 2023, ta tabbatar da nasarar ta ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, 2023."

'Yan mazabar sun yi zargin cewa:

"Dabi'un da sanatar ta nuna sun sanya al’ummar Kogi ta Tsakiya cikin kunya, tare da rage martabar majalisar dattawa da kuma ƙin bin ka’idojin dimokuraɗiyya a Najeriya.”

INEC, Natasha ba su magantu kan korafin ba

Jaridar The Nation ta rahoto masu shigar da korafin sun ƙara da cewa:

“Mun tabbatar da cewa sama da rabin masu zaɓe da ke a mazabar Kogi ta Tsakiya sun sa hannu a wannan ƙorafi.
"Saboda haka, muna buƙatar hukumar INEC ta gaggauta aiwatar da matakan kundin tsarin mulki domin tunbuke Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga ofis, tare da bayyana kujerarta a matsayin babu kowa a kanta.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Zanga zanga ta barke kan takaddamar Natasha, an samu bayanai

Har yanzu, INEC ba ta fitar da wata sanarwa game da ƙorafin ba, haka kuma, har yanzu Sanata Akpoti-Uduaghan ba ta yi wata magana a hukumance game da ƙorafin ba.

A ƙarƙashin dokokin Najeriya, dole ne hukumar ta tantance sahihancin sa hannun masu ƙorafin sannan ta shirya kada kuri’a kafin a kammala tsarin tunbuke dan majalisa daga ofis.

'Ba na jin tsoron kiranye' - Sanata Natasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ba ta damu ba kan ƙoƙarin wasu 'yan mazabarta na neman tunbuke ta daga majalisar dattawa.

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa bata da wata fargaba game da yunƙurin da aka fara don yi mata kiranye daga majalisar.

A cewarta, wasu ƴan siyasa ne ke jagorantar shirin kiranye a kanta, amma hakan ba zai taɓa yin tasiri a kanta ko a kujerarta ba, domin ta na tafiya a kan turba ta gaskiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng