'Matar Tinubu na Cewa Kiristocin Arewa Musulmai Sun Juya Masa Baya,' Dalung
- Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya ce akwai yunkurin rarraba yankin Arewa ta hanyar rabuwar kai tsakanin Musulmai da Kiristoci
- Dalung ya caccaki matakin wasu shugabannin Kiristoci da ke kokarin marawa Tinubu baya bayan sun yi adawa da tikitin Musulmi da Musulmi
- Solomon Dalung ya ce ya fi son hadin gwiwa da Musulman Arewa wajen fitar da dan takara daga Kudu domin kalubalantar Tinubu a 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon ministan wasanni a Najeriya, Solomon Dalung, ya bayyana ra'ayinsa kan yadda siyasar yankin Arewa ke tafiya bayan zaben 2023.
A cewarsa, an rarraba yankin ne sakamakon yadda Kiristocin Arewa suka yi yakin neman zabe da dalilin addini a baya, amma yanzu wasu daga cikinsu na goyon bayan Tinubu.

Kara karanta wannan
'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da Solomon Dalung ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalung ya ce ya yi jawabin ne yayin hira da jaridar Punch, ya caccaki matakin wasu shugabannin Kiristoci da ke kokarin marawa Tinubu baya bayan sun yi watsi da shi a baya.
Solomon Dalung a kan Kiristocin Arewa
Dalung ya zargi wasu shugabannin Kiristocin Arewa da nuna son zuciya da rashin adalci a siyasa.
A cewarsa, a zaben 2023 sun yi yaki da tikitin Musulmi da Musulmi, amma yanzu su na karbar Tinubu bayan ya fuskanci adawa daga Musulmai.
Tsohon ministan ya ce:
"Idan har Kiristocin Arewa na da gaskiya, kamata ya yi su hada kai da Musulmai su fitar da dan takara daga Kudu don kayar da Tinubu, ba wai su rika karbar kudi su sauya ra'ayi ba."

Kara karanta wannan
Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027
Dalung ya zargi matar Tinubu da raba kai
Dalung ya ce matar Shugaban kasa, Remi Tinubu, tana amfani da Kiristocin Arewa domin tallafa wa siyasar mijinta.
A cewarsa, tana bin shugabannin Kiristoci tana kokarin jawo su da hujjar cewa Musulman Arewa sun watsar da Tinubu, don haka Kiristoci su goyi bayansa.
Ya ce wannan yunkuri yana nuna yadda wasu Kiristoci ke nuna fuska biyu a siyasa, don haka ba zai yarda da hakan ba.

Asali: Facebook
Dalung ya bukaci hadin kai a siyasa
Dalung ya ce fiye da komai, yana ganin ya fi dacewa ya hada kai da Musulman Arewa domin fitar da dan takara daga Kudu.
Tsohon ministan ya ce:
"Idan Musulmai suka ce an yaudare su kuma sun gane kuskurensu, ni Kirista ne kuma Littafina yana koyar da yafiya. Zan yafe musu kuma mu hadu mu fitar da madadin Tinubu."
Dalung ya jaddada cewa zai fi son tsayawa kan bakansa na adawa da tikitin Musulmi da Musulmi fiye da bin tafiyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya hango faduwar Tinubu a 2027, ya kwatanta hakan da lamarin Jonathan
Binani ta gana da shugaban SDP na kasa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar 'yar takarar APC a zaben gwamnan jihar Adamawa ta gana da shugaban SDP na kasa.
Shehu Musa Gabam ya ce sun tattauna abubuwa masu muhimmanci da Aisha Binani da suka shafi siyasar Najeriya da cigaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng