Sule Lamido Ya Fadi Hanya 1 da Jam'iyyun Adawa Za Su ba Tinubu Wahala a 2027

Sule Lamido Ya Fadi Hanya 1 da Jam'iyyun Adawa Za Su ba Tinubu Wahala a 2027

  • Tsohon gwamna, Sule Lamido ya ce fushi da jin haushi ba zai taimaka wa 'yan adawa su kayar da Bola Tinubu ba a siyasa
  • Ya bukaci dukkan tsofaffin shugabannin PDP da suka bar jam'iyyar su dawo su hada kai don ceton Najeriya
  • Lamido ya ce PDP kadai ke da cikakken karfi da dama na karbe mulki idan 'ya'yanta suka hade su zama tsintsiya madaurinki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa kan zaben 2027.

Lamido ya bayyana cewa ba za a iya kayar da Shugaba Bola Tinubu ta hanyar fushi da zuciya ba.

Sule Lamido ya shawarci yan adawa kan yakar Tinubu a 2027
Sule Lamido ya soki yadda ake gudanar da adawa a yanzu. Hoto: Sule Lamido, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Lamido ya kanbama tasirin PDP a Najeriya

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga wasu kungiyoyi na mambobin PDP daga Jigawa da suka halarci karin kumallo tare da shi, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

"Ba za ku tabuka komai ba," Ministan Tinubu ya yi watsi da kwancen adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamido ya dage cewa PDP ce kadai ke da karfin da zai iya dawo da mulki idan ta hada kan mambobinta ta zama jam’iyya mai karfi da tsari.

Ya bayyana cewa dukkan jagorori da manyan ‘yan siyasa na jam’iyyun adawa, banda PDP, sun fito daga PDP ne kuma sun ci gajiyar mukamai a matakai daban-daban kafin su fice.

Tsohon gwamnan ya bukaci irin su Nasiru El-Rufai, Peter Obi, Rabi’u Kwankwaso da sauran su da su dawo jam’iyyar PDP su hada karfi da tsofaffin shugabanni domin ceton Najeriya.

A cewarsa:

“Ba za a iya yakar Tinubu da fushi da jin haushi ba. Ya fi dacewa shugabannin jam’iyyun adawa su dawo gida su hada kai da danginsu.
“Ku dawo gida, babu kunya cikin hakan, ku hade da iyalan ku na gaskiya da kuka tafiyar da mulki daga 1999 zuwa 2015.
Sule Lamido ya fadi hanyar yakar Bola Tinubu a 2027
Sule Lamido ya nuna damuwa kan yadda ake adawar fushi da hassada a yanzu. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Twitter

Lamido ya kawo shawara kan zaben 2027

Lamido ya ce ya kamata a yi zama na musamman wurin duba halin da Najeriya ke ciki domin ceto ta.

Kara karanta wannan

Aiki zai dawo sabo: Gwamnoni 12 za su maka Tinubu a kotu kan Fubara

Ya kara da cewa:

“Ya kamata mu zama masu nazari da gaskiya, mu duba halin da kasar ke ciki kafin gwamnati ta yanzu, shin muna da sauki yanzu?”

Ya yabawa shugabannin jam’iyyar da mambobi da ‘yan majalisa da suka tsaya a jam’iyyar, yana cewa sun nuna kishin kasa da hangen nesa.

Wani ɗan PDP ya tattauna da Legit Hausa

Dan a mutun PDP a Gombe, Sani Muhammad ya ce akwai matsala kan yadda yan jam'iyyun adawa ke tunkarar Tinubu.

"Ya kamata a sauya yadda ake gudanar da adawa saboda wannan tsari ba zai kai ga kwace mulki cikin sauki ba."

- Cewar Sani

Daga bisani ya shawarci shugabannin PDP da su hada kai domin samun adawa mai karfi kafin zaben 2027.

Lamido ya soki El-Rufai bayan komawa SDP

Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Nasir El-Rufai ba ya da darajar shugabanci da zai iya janyo ‘yan PDP su bi shi SDP ba.

Tsohon gwamnan ya ce El-Rufai bai cancanci gayyatar manyan ‘yan adawa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba domin ba shi da kishin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel