Tinubu Ya Ware Ƴan APC a Jiha 1, Ya ba Su Buhunan Shinkafa 7,000 saboda Ramadan

Tinubu Ya Ware Ƴan APC a Jiha 1, Ya ba Su Buhunan Shinkafa 7,000 saboda Ramadan

  • Shugaba Bola Tinubu ya bai wa mambobin jam’iyyar APC a Zamfara buhunan shinkafa 7,000 a matsayin kyautar azumin Ramadan
  • Bello Matawalle ne ya kaddamar da rabon shinkafar a Gusau wanda shugaban APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani ya wakilce shi
  • An yi rabon ne don rage tsananin matsin tattalin arziki da mambobin jam’iyya da talakawa ke fuskanta a jihar Zamfara
  • Matawalle ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da addu’a don zaman lafiya da hadin kai a jihar da kasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ba da gudunmawar buhunan shinkafa 7,000 ga mambobin jam’iyyar APC a Zamfara a matsayin kyautar Ramadan.

Wannan na daga cikin tallafi da shugaban Najeriyan ya bayar duba da halin da ake ciki musamman a wannan wata na Ramadan.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

Tinubu ya gwangwaje ƴan APC a Zamfara da abin alheri
Bola Tinubu ya ba shugabannin APC buhunan shinkafa a Zamfara. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Matawalle ya jagoranci raba shinkafa a Zamfara

Sakataren watsa labarai na APC a jihar, Yusuf Idris, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau yau Asabar 22 ga watan Maris, 2025, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙaramin ministan tsaro, Dr Bello Matawalle ya kaddamar da rabon tallafin a jiya Juma’a a Gusau, babban birnin jihar.

Wakilin Matawalle kuma shugaban APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani shi ya mikawa shugabannin jam’iyyar shinkafar a sakatariyar APC.

Ya bayyana cewa kyautar ta fito ne daga Shugaba Tinubu da kansa domin rage radadin matsin tattalin arziki ga mabukata da mambobin APC.

Matawalle ya ce za a raba buhunan shinkafar kyauta ga shugabannin jam’iyya na matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu.

Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya da daidaito a jihar da kasa baki daya.

A cewarsa, gwamnatin tarayya karkashin Tinubu na daukar matakai na dakile ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifukan da ke addabar yankin.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Ya ce:

“Wannan tallafin yana nuna godiya ga jajircewar shugabannin APC na jihar wajen hada kan jam’iyya da inganta ci gabanta."
“A matsayinmu na shugabanni, za mu ci gaba da tallafawa jam’iyya ta kowanne fanni don cimma nasara.”
Tinubu ya gwangwaje yan APC a Zamfara
Bola Tinubu ya ba yan APC a Zamfara buhunan shinkafa domin azumin Ramadan. Hoto: Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Rokon da Matawalle ya tura ga 'yan APC

Matawalle ya kuma yi kira da a ci gaba da samun fahimta da hakuri a tsakanin mambobin jam’iyyar domin hada kai da zaman lafiya.

Sakataren jam’iyyar APC na jihar, Ibrahim Dangaladima, wanda ya karbi shinkafar a madadin jam’iyyar, ya gode wa Tinubu da Matawalle.

Dangaladima ya ce tallafin ya zo a daidai lokacin da mutane ke cikin matsanancin bukatar abinci saboda halin rayuwa.

Rivers: Matawalle ya fadi shirin sojoji

Mun ba ku labarin cewa karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya goyi bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sanya dokar ta ɓaci a Rivers.

Matawalle ya bayyana cewa matakin ya zama wajibi duba da yadda rikicin jihar ke kawo tangarɗa ga harkokin mulkin dimokuraɗiyya.

Tsohon gwamnan ya nuna cewa sojoji suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kare muhimman kayayyakin gwamnati daga barazanar tsageru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng