Shekarau Ya Fadi Abin da Zai Faru bayan Haduwar El Rufai, Atiku kan Kifar da Tinubu
- Tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce haɗin gwiwar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Peter Obi ba za ta kayar da APC ba a 2027
- Shekarau ya ce babu ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyun adawa da ke cikin wannan haɗin gwiwar da ke da cikakken goyon bayan jam’iyyarsa
- Ya bayyana cewa wannan haɗin kai ba wata cikakkiyar haɗewar jam’iyyu ba ce, domin ba doka ta amince da su a matsayin jam’iyya ɗaya ba
- Shekarau ya ce ba za a iya samun tasiri a zaɓe ba, sai an haɗa da dukkan shugabannin jam’iyyun adawa a matakin ƙasa da jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa kan zaben 2027.
Shekarau ya ce babu wata haɗaka da za ta iya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Asali: Twitter
Shekarau ya magantu kan alakarsa da Kwankwaso
A cikin wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar, Shekarau ya ce wannan haɗin gwiwar ba ta haɗa da shugabancin kowace jam’iyya ba, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanann na zuwa ne bayan Sanata Ibrahim Shekarau ya ce yana da kyakkyawar alaka da Rabiu Kwankwaso da kuma Abdullahi Ganduje duk da bambancin siyasa.
Shekarau ya ce babu abin da zai hana shi zama inuwa daya da Kwankwaso saboda har yanzu suna gaisawa kan wasu lamura.
Shekarau ya magantu kan hadakar jam'iyyun adawa
Wannan matsayi na Shekarau ya zo ne kwana biyu bayan da wasu jiga-jigan 'yan adawa su ka soki gwamnatin tarayya kan rikicin siyasar Jihar Rivers.
Malam ya ce wannan haɗin kai kamar gangamin wasu mutane ne masu girma, amma hakan ba zai zama haɗin jam’iyya ba.
A cewarsa:
“Haɗuwar wasu manyan ‘yan adawa abu ne mai kyau, amma babu wanda ke wakiltar jam’iyyarsa cikin wannan haɗin da ake kira ‘coalition.’”

Asali: Facebook
Shekarau ya yi kokwanton tasirin adawa a majalisa
Shekarau ya kara da cewa ba za a kira su haɗin jam’iyyu ba, domin doka ce kawai ke bayar da damar haɗa jam’iyyu ta hukuma.
Ya ce amincewar Majalisar Tarayya da dokar ta-ɓaci da Tinubu ya sanya ta bayyana cewa ba su da iko a majalisa ko kan jam’iyyun adawa.
Ya ce:
“Ba za a iya samun tasiri a zaɓe ba, sai idan an haɗa da dukkanin shugabanni na jam’iyyun adawa a kowane mataki.”
Shekaru ya fadi dalilin kafa sabuwar tafiyarsu
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya nuna cewa sabuwar tafiyarsu na son zaburar da jama'a kan shugabanci na gari.
Sanata Shekarau ya fadi haka ne bayan ziyarar da ya kai birnin Abeokuta domin zama da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.
Tsohon gwamnan ya ce kasar nan, musamman Arewa da su ka fito na fama da matsaloli da ke bukatar a magance su ba tare da bata lokaci ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng