"Ba za Ku Tabuka komai ba," Ministan Tinubu Ya Yi Watsi da Kwancen Adawa

"Ba za Ku Tabuka komai ba," Ministan Tinubu Ya Yi Watsi da Kwancen Adawa

  • Karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata, ya ce caccaki kawancen adawa tsakanin Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da Peter Obi
  • Ya bayyana yunkurin jiga jigan 'yan adawar da cewa ba zai tabuka komai wajen cutar da siyasar Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa ba
  • Ministan ya kara da cewa ayyukan Bola Tinubu, ciki har da sanya dokar ta baci a jihar Ribas ya nuna kwarewar shugabanci da iya siyasarsa

Jihar KanoKaramin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata, ya bayyana yunkurin kawancen jam'iyun adawa da cewa ba zai yi tasirin komai ba.

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i; da tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi sun shirya kalubalantar Bola Tinubu.

Atiku
Ata ya caccaki kawancen 'yan adawa Hoto: Nasir El-Rufa'i/Bayo Onanuga/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Yusuf Ata ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Seyi Olorunsola, ya raba ga manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Ministan gidaje ya caccaki El-Rufa’i da Atiku

The Guardian ta wallafa cewa Ministan ya bayyana Atiku, Obi da El-Rufa’i, wadanda ya bayyana a matsayin “yan siyasa uku da ke ta faman yawo ba tare da tsayayyen matsaya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shawarce su da su farka daga barcin siyasar su, domin kuwa ‘yan Najeriya sun riga sun tabbatar da nagartaccen shugabanci a karkashin gwamnatin APC ta yanzu.

Ata ya ce:

"Kasar nan ta wuce zamanin gwaji a shugabanci, kuma ‘yan siyasar da ba su da wata manufa face amfani da tunzura jama’a ba za su samu goyon baya ba.”

Ministan ya yabawa shugabancin Tinubu

A cewar karamin Ministan, Shugaba Bola Tinubu yana kan turbar da ta dace wajen sauya fasalin Najeriya domin ta tarar da takwarorinta a duniya.

Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulki a 2023, Tinubu ya aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da na siyasa masu muhimmanci domin daidaita Najeriya.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Tinubu
Ata ya ce ayyukan Tinubu sun tabbatar da kwarewarsa ga 'yan Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Yusuf Ata ya jinjina wa Tinubu kan nagartaccen jagorancinsa, bin doka da oda, da kuma tafiyar da harkokin kasa bisa gaskiya da adalci.

Ata ya bayyana wasu manyan ayyukan Tinubu

Ata ya ce Shugaban kasa ya gaggauta shawo kan rikicin siyasa da ya kunno kai a jihar Ribas, kuma hakan shaida ce ta kwarewarsa wajen mulki da kuma kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya.

Ministan ya kuma yi suka ga kawancen Atiku, Obi da El-Rufa’i, yana mai cewa hadin gwiwar su ba ta da tushe, kuma ba za ta samu karbuwa a idon ‘yan Najeriya ba.

Ya kara da cewa:

"Shugaba Bola Tinubu ne shugaba mafi adalci da gaskiya da Najeriya ta samu a wannan lokaci.
"Gwamnatin yanzu na mayar da hankali wajen kawo ci gaba mai ma’ana, kuma ba za ta bari ‘yan siyasar da ke neman mulki ba tare da wata manufa mai karfi ba su raba ta da tafiyarta ba."

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Ministan Tinubu ya caccaki Obi

Yusuf Ata ya zargi Peter Obi da rura wutar bambancin kabila da addini, yana mai cewa dabarunsa na bata sunan shugabanni nagari irin su Tinubu ba za su kai shi ga nasara ba.

Ya kwatanta kawancen da wata kungiya ce ta ‘yan siyasa da suka rasa dangantaka da al’umma kuma ke kokarin nemo suna a idon jama’a.

'Yan adawa na shirin kifar da Tinubu

A wani labarin, mun ba ku labarin cewa manyan ‘yan siyasa a Najeriya sun sake haduwa a birnin tarayya Abuja domin tsara dabarun kwace mulki daga hannun shugaba Bola Tinubu.

Tsohon Mataimaki Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC da suka koma adawa sun kafa kawance domin kalubalantar mulkin Tinubu a babban zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng