Wike Ya Sake Samun Nasara, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Rikicin Sakataren PDP na Ƙasa

Wike Ya Sake Samun Nasara, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Rikicin Sakataren PDP na Ƙasa

  • Kotun Koli ta raba gardama kan rikicin kujerar sakataren PDP da aka shafe dogon lokaci ana yi tsakanin Samuel Anyanwu da Ude-Okoje
  • A zaman yau Juma'a, kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta tabbatar da Anyanwu, na kusa da Nyesom Wike a matsayin halastaccen sakatare
  • Wannan hukunci ya soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Enugu, wadda ta tsige Anyanwu daga matsayinsa a majalisar NWC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun Koli ta Najeriya ta bayyana Samuel Anyanwu, wanda ke da kusanci da Ministan Abuja, a matsayin halastaccen sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.

Sanata Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun shafe lokaci suna gwabza rikici kan wannan matsayi, lamarin da ya haddasa rabuwar kai a tsakanin shugabannin jam’iyyar.

Ude Okoye da Anyanwu.
Kotun Koli ta ayyana Samuel Anyanwu a matsayin sakataren ƙasa na jam’iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Ude-Okoye na da goyon bayan wasu daga cikin ƙusoshin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ta ƙasa watau NWC.

Kara karanta wannan

Jama'a sun ɓarke da azababben faɗa a watan azumi, an kashe tsohon mai mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin sakatare ya raba kawunan ƴan PDP

Ude-Okoye ya samu goyon bayan wasu sassa na PDP sakamakon hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu, wacce ta tabbatar da cire Anyanwu daga mukaminsa.

Sai dai a hukuncin da Kotun Koli ta yanke ranar Juma’a, kwamitin alkalai guda biyar sun bayyana cewa Sanata Anyanwu ne halastaccen sakataren PDP na ƙasa.

Kwamitin akalan ya yi bayanin cewa batun shugabanci ko zama mamba a cikin wata jam’iyya lamari ne da ya shafi cikin gida, ba abin da kotu za ta tsoma baki ba.

Kotun ƙoli ta yanke hukuncin karshe

A hukuncin da Mai Shari’a Jamilu Tukur ya karanto, Kotun Koli ta ce babu wani dalili da zai ba kotu damar shiga cikin al’amuran cikin gida na jam’iyya.

Kotun koli ta ce wurin da kotu ke da hurumin tsoma baki a harkokin jam'iyya shi ne idan kundin tsarin mulki ya ba ta dama ko kuma aka saɓa wata doka ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta ceto Sanata Natasha daga barazanar raba ta da kujerarta

Yadda rikicin sakataren PDP ya faro

Rigima kan kujerar sakataren jam'iyyar PDP ya taso ne bayan Anyanwu ya bar matsayinsa don yin takarar gwamna a jihar Imo, inda ya sha kaye a hannun APC

Sai dai bayan ya sha kasa a zaɓen, Sanaya Anyanwu ya yi ƙoƙarin komawa kan kujerarsa ta sakataren PDP na ƙasa, lamarin da ya ƙara hargiza jam'iyyar.

A ranar 20 ga Disamba, 2024, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jiha da ta tsige Anyanwu.

Sannan kuma ta tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakataren PDP na ƙasa, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Sanata Anyanwu bai yarda da hukuncin ba, ya garzaya Kotun Koli don neman dakatar da aiwatar da hukuncin tare da ɗaukaka ƙara.

A yau Juma'a, kotun kolin ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP na ƙasa, tare da soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

PDP ta buƙaci a kama sakataren APC

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta fito ta bayyana ɓacin ransa kan kalaman Ajibola Basiru, sakataren APC wanda ya nemi a sa dokar ta-baci a jihar Osun.

PDP ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta cafke Sanata Basiru bisa wannan magana da ya yi, domin barazana ce ga tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng