An Nemi Kama Sakataren APC kan Yunkurin Dakatar da Gwamnan PDP a Osun

An Nemi Kama Sakataren APC kan Yunkurin Dakatar da Gwamnan PDP a Osun

  • Jam’iyyar PDP ta bukaci a kama sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru kan kiran da ya yi na a ayyana dokar ta-baci a Osun
  • Sanata Ajibola Basiru ya bayyana cewa ya kamata shugaban kasa fadada dokar ta-bacin da aka kafa a Rivers zuwa jihar Osun
  • A karkashin haka, PDP ta zargi APC da shirya haddasa rikici domin kwace mulki ta bayan fage bayan shan kaye a zaben jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta da kiraye-kirayen da Sanata Ajibola Basiru na APC ya yi na kafa dokar ta-baci a jihar Osun.

Basiru ya yi kiran ne bayan shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers, lamarin da ya jawo da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar jihar.

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

Ganduje
PDP ta bukaci a kama sakatren APC na kasa. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje|Official PDP
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa PDP ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta cafke Basiru bisa wannan matsaya da ya dauka domin tattabar da tsaro a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin siyasar Ribas da tasirinsa a Osun

Tun da farko, wasu 'yan APC reshen Osun sun nuna goyon baya ga kiran Basiru na a kafa dokar ta-baci a jihar.

A cewarsu, rikicin siyasa da ke gudana a Osun ya kai wani mataki mai hadari da ke bukatar matakin gaggawa domin tabbatar da doka da oda.

A ‘yan makonnin da suka gabata, rikicin siyasa a jihar ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida, yayin da ma’aikatan kananan hukumomi suka daina aiki sakamakon rashin tsaro.

PDP ta caccaki APC da Sanata Basiru

Da yake mayar da martani kan wannan batu, kakakin PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce Basiru ya na kokarin tayar da zaune tsaye a jihar Osun domin cimma muradunsa na siyasa.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Ologunagba ya ce:

“Sanata Basiru mutum ne da aka san shi da haddasa tarzoma a Osun. Kuma muna da labarin cewa yana shirin tsayawa takarar gwamna a 2026.
"Idan gwamnati na da niyyar tabbatar da zaman lafiya a kasar nan, dole ne a kama shi yanzu.”

Ya kara da cewa APC na kokarin haddasa rikice-rikice a sassan Najeriya domin samun hujjar kwace iko a wasu jihohi.

“Sun riga sun tsara yadda za su tsorata ‘yan Najeriya tare da cafke su ba tare da dalili ba, amma duk wani yunkurinsu ba zai yi nasara ba,”

- Debo Ologunagba

Shugaban PDP
Shugaban PDP na kasa. Hoto: Official PDP
Asali: Facebook

Duk da wannan suka da PDP ke yi, Basiru bai sauya matsayarsa ba. Ya ci gaba da yabawa shugaba Tinubu kan matakin da ya dauka a Rivers.

Sakataren jam'iyyar APC ya bayyana cewa kamata ya yi a dauki irin wannan mataki a Osun domin gyara tsarin shugabanci na kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Rivers: 'Yan adawa sun kalubalanci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin 'yan adawa sun hadu a birnin tarayya Abuja sun kalubalanci matakin Bola Tinubu na dakatar da gwamnan Rivers.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya jagoranci taron ya bayyana cewa dakatar da zababben gwamna ya saba kundin tsarin mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel