Dakatar da Fubara: Sanata Ya Fara Gangamin Yakar Bukatar Tinubu a Majalisa

Dakatar da Fubara: Sanata Ya Fara Gangamin Yakar Bukatar Tinubu a Majalisa

  • Tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, ya ce dokar ta-baci da Bola Tinubu ya kafa a jihar Rivers ya sabawa kundin tsarin mulki
  • Sanata Seriake Dickson ya ce zai hada kai da abokan aikinsa, a hana majalisar dattawa amincewa da matakin shugaban kasar
  • Bayan haka, ya kuma yi kira ga Bola Tinubu da ya yi koyi da Goodluck Jonathan wajen tafiyar da harkokin mulki da siyasa lami lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya yi Allah-wadai da dokar ta-baci da shugaba Bola Tinubu ya kafa a jihar Rivers.

Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa matakin da shugaban kasar ya dauka wata hanya ce ta karbe mulki da karfi a jihar.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Seriake Dickson
Sanata Dickson zai yi adawa da dakatar da gwamna Fubara. Hoto: @iamHSDickson
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa Dickson ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin hirar, Sanata Dickson ya ce an dauki matakin ba bisa ka’ida ba kuma ya sabawa kundin tsarin mulki.

Yunkurin hana amincewa da matakin Tinubu

Tsohon gwamnan ya ce zai hada kai da wasu Sanatoci domin hana majalisar dattawa amincewa da wannan doka, yana mai cewa dole ne a tantance ko matakin ya dace da tsarin mulki ko a’a.

"Ba za a iya tattauna batun dokar ta-baci ba sai an samu a kalla sanatoci 73 da kuma 'yan majalisar wakilai 240 sun hallara a zaman majalisa.
"Idan hakan bai faru ba a cikin kwana biyu, to lamarin zai koma yadda yake,"

- Sanata Seriake Dickson

Ya kara da cewa yawancin sanatoci, musamman tsofaffin gwamnonin da suka san muhimmancin kare dimokuradiyya, ba za su amince da wannan mataki ba.

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Kiran Tinubu da ya yi koyi da Jonathan

Sanata Dickson ya tunatar da yadda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya tafiyar da dokar ta-baci a jihohin Borno, Adamawa da Yobe a lokacin da Boko Haram ta addabi yankin.

Dickson ya ce shugaba Jonathan ya sanya dokar ta-baci ba tare da dakatar da gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohin ba.

Premium Times ta wallafa cewa Sanatan ya ce:

"Lokacin da Jonathan ya kafa dokar ta-baci saboda Boko Haram, an yi masa shawarwari daban-daban, wasu na cewa a dakatar da gwamnoni.
"Amma ya fahimci cewa shi shugaba ne na kowa, don haka bai dakatar da shugabanni ba."

Dickson ya ce babban dalilin dokar ta-baci shi ne karfafa gwamnatoci da ke kan mulki domin su shawo kan matsala, ba wai a dakatar da su ba.

Ya bukaci shugaba Tinubu da ya yi koyi da salon jagorancin Jonathan, domin kare dimokuradiyya da kuma mutunta tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'laifin' Wike

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Rikicin Rivers: Gwamnati ta wanke Wike

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta wanke ministan Abuja, Nyesom Wike kan dokar ta baci da aka sanya a jihar Rivers.

Ministan shari'a na kasa ya bayyana cewa duk abin da ya faru a jihar har ya jawo sanya dokar ta baci laifin gwamnan jihar ne, Siminalayi Fubara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng