Tsohon Hadimin Jonathan Ya Dauko Zancen Tsige Tinubu kan Dakatar da Gwamnan Ribas

Tsohon Hadimin Jonathan Ya Dauko Zancen Tsige Tinubu kan Dakatar da Gwamnan Ribas

  • Tsohon kakakin Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara, Reuben Abati, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da watsi da kundin tsarin mulki
  • Ya bayyana cewa Bola Tinubu ba shi da ikon dakatar da zababbun gwamnoni ko ‘yan majalisar jiha
  • Dr. Abati ya fadi girman kuskuren da Tinubu ya tafka, inda ya yi fatan 'yan majalisa za su cire tsoro wajen fara yunkurin tsige shugaban

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon mai ba wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara, Reuben Abati, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da take kundin tsarin mulkin Najeriya wajen sanya dokar ta baci a Ribas.

Dr. Abati ya bayyana cewa Shugaban Kasa ba shi da ikon dakatar da zababben gwamna ko ‘yan majalisar jiha, duk da cewa yana iya jingina hakan da wani sashe na kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

Tinubu
An zargi Tinubu da take dokar kasa Hoto: @DOlusegun, @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da ya yi da Arise TV, wacce Journalist KC ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon hadimin shugaban kasar ya zargi Tinubu da mulkin kama karya da danniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shugaban kasa ya take sashen da ya dogara da shi wajen dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar.

Tinubu: An bayyana sharudan dakatar da gwamna

Daily Post ta wallafa cewa Abati ya ce sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana takamaiman sharudan da za su jawo a iya sanya dokar ta baci a wata jiha.

Ya ce:

"Wannan sashe ya na bayyana cewa ana iya sanya dokar ta baci ne idan kasar na fuskantar barazanar yaki ko kuma akwai barazanar yaki mai zuwa. Shin, Najeriya na fuskantar barazanar yaki a Jihar Ribas?

Ya ci gaba da cewa:

"Sashen ya kuma bayyana cewa idan rikici mai tsanani ya taso a wani bangare na ƙasar da zai iya jefa Najeriya cikin ruɗani, shugaban kasa yana da ikon ɗaukar mataki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

"Idan gwamnan jihar bai yi gaggawar magance matsalar ba ko kuma bai nemi Shugaban Kasa ya shiga don kare muradun ƙasa ba, to Shugaban Kasa na iya sanya dokar ta baci.”

An ilimantar da Tinubu kan dokar ta baci

Abati ya bayyana cewa, Sashe na 305 na kundin tsarin mulki ya na nuni da cewa shugaban kasa zai fitar da sanarwa, wacce za a wallafa, sannan za a tura ta zuwa ga majalisar tarayya.

Tinubu
Ana fatan majalisa za ta tsige Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce:

"Idan majalisar tarayya ta na aiki, dole ne ta yi aiki a kan takardar a cikin sa’o’i 48. Idan ta na hutu, dole ne ta yi aiki a cikin kwanaki 10."
Idan majalisar tarayya ba ta amince da wannan sanarwa ba, to za ta kada kuri’a kuma matakin zai rushe. Dole ne a sami rinjayen kuri’un Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai."

"Tinubu ya karya doka a Ribas," Abati

Tsohon hadimin Jonathan ya bayyana cewa Majalisar zartarwa ta tarayya ba ta da iko na yin katsalandan wajen samar da dokoki a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Rivers: Ƴan majalisa sun fadi matsayarsu kan dokar ta ɓaci, sun fadi mai laifi

Ya ce:

"Sashe na 11 na kundin tsarin mulki yana cewa, idan an sanya dokar ta baci, kawai Majalisar Tarayya ce ke da ikon samar da dokoki ga Majalisar dokokin jiha."
Yanzu, Shugaba Tinubu yana kokarin kwace ikon yin dokoki ga Majalisar dokokin jihar Ribas. Wannan babban laifi ne da zai iya kai shi ga tsige shi."

Ya ƙara da cewa:

"Ban san ko Majalisar tarayya za ta sami ƙwarin gwiwar ko dai ta yi watsi da sanarwar da aka wallafa ko kuma ta fara shirin tsige shi saboda take kundin tsarin mulkin Najeriya ba."

Ribas: Majalisa ta kare Tinubu

A baya, kun samu labarin cewa Majalisar wakilai ta ce sai da shugaba Bola Tinubu ya tattauna da majalisar kasar nan kafin a yanke wannan hukunci kan sanya dokar ta baci a jihar Ribas.

Mai magana da yawun majalisa, Akin Rotimi ya kuma bayyana cewa an gudanar da zaman tare da manyan shugabannin majalisar, ciki har da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng