Fubara Ya Yi Bayanin Farko bayan Tinubu Ya Dakatar da Shi daga Gwamna

Fubara Ya Yi Bayanin Farko bayan Tinubu Ya Dakatar da Shi daga Gwamna

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya ce ya yi kokarin tabbatar da doka da oda a Jihar Rivers duk da rikicin siyasa
  • Ya bayyana cewa majalisar dokokin jihar ta taka rawa sosai wajen hana samun daidaito da ci gaban lamura
  • Duk da dakatar da shi da Bola Tinubu ya yi, Fubara ya bukaci mutanen Rivers su ci gaba da bin doka da oda a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bukaci al'ummar jihar su zauna lafiya tare da bin doka yayin da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da majalisar dokokin jihar.

Fubara ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa kundin tsarin mulki don kare mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

Fubara
Fubara ya yi bayani bayan Tinubu ya dakatar da shi. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Sakataren yada labaran gwamnan jihar ne ya fitar da sanarwa kan jawabin da Fubara ya yi a shafinsa na Facebook jim kadan bayan dakatar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Simi Fubara ya yi kokarin yin sulhu

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawan gwamnatinsa, ya kasance ya na aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da matsalolin siyasa, ya ci gaba da yin aiki don tabbatar da tsaro da inganta walwalar mutanen jihar Rivers.

Ya kara da cewa bayan shugaban kasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya bi yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karbar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar doka da oda.

Fubara ya jefi majalisar dokokin Rivers da zargi

Gwamnan ya ce duk da kokarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, 'yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuradiyya da ci gaban mutanen Rivers, amma majalisar na hana hakan ta tabbata.

A cewarsa, duk da sabanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don cigaban jihar.

Fubara ya bayyana cewa duk da kalubalen siyasa, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Kiran gwamna Fubara ga al’ummar Rivers

Duk da dakatar da shi da aka yi, gwamnan ya bukaci mutanen Rivers da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntubar hukumomin da suka dace don kare dimokuradiyya da tabbatar da cigaban jihar.

Punch ta wallafa cewa gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

Rivers: Ƴan majalisa sun fadi matsayarsu kan dokar ta ɓaci, sun fadi mai laifi

"Al’ummar Rivers mutane ne masu juriyar jure wahala, kuma za su fuskanci wannan matsala da basira, hakuri, da aminci da bin tafarkin dimokuradiyya."

Fubara a matsayin gwamnan Ribers

Tun farkon hawan Fubara gwamna a jihar Rivers yake samun sabani da wanda ya gada, Nyesom Wike kan wasu ra'ayoyi nasu da suka bambanta na siyasa.

A lokuta da dama, an sha samun cece-kuce da kai ruwa rana tsakanin gwamnan da majalisar dokokin jihar, inda ake zargin hannun Wike a duk abin da ke faruwa a rikicin siyasar jihar.

Idan ba ku manta ba, Wike a halin yanzu minista ne a majalisar ministocin shugaba Tinubu duk da kasancewarsa mamba a jam'iyyar PDP.

Akwai masu hasashen cewa, Wike na yiwa PDP da Fubara zagon kasa ne a shirin zaben 2027 mai tafe don sharewa shugaban kasa Bola Tinubu a zaben.

Duk da akwai kamshin gaskiya a maganar, Wike ya sha musanta abin da ake hange tattare da shi, inda ya ke yawan bayyana matsayarsa ta siyasa.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya dauko zancen tsige Tinubu kan dakatar da Gwamnan Ribas

PDP ta yi Allah wadai da dakatar da Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya yi a wani jawabi.

PDP ta ce shugaban kasa ba shi da ikon dakatar da gwamna a bisa doka, saboda haka jam'iyyar ta bukaci Bola Tinubu ya janye matakin da ya dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya habaka labarin nan ta hanyar fadada bayani kan rikicin Fubara da Wike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng