Bayan Shekara 2, Buba Galadima Ya Fadi Wanda Ya Yi Nasara a Zaben Gwamnan Legas

Bayan Shekara 2, Buba Galadima Ya Fadi Wanda Ya Yi Nasara a Zaben Gwamnan Legas

  • Daya daga cikin jagororin NNPP, Alhaji Buba Galadima ya zargi APC da murde zaben gwamnan jihar Legas da aka gudanar a shekarar 2023
  • Ya bayyana cewa magoya bayan PDP sun yi tururuwar zuba wa Abdul-Azeez Olajide Adediran, da aka fi sani da Jandor kuri'a, amma APC ta kwace
  • Kalamansa na zuwa ne kwanaki kadan bayan Jandor ya tattauna da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, sannan ya sauya sheka zuwa APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar LagosJagora a NNPP, Alhaji Buba Galadima, ya bayyana cewa ɗan takarar gwamna na PDP a Legas, Abdul-Azeez Olajide Adediran, da aka fi sani da Jandor, ne ya lashe zaɓen gwamna na 2023.

Bayaninsa na zuwa ne kwanadi kadan bayan tsohon dan takarar, Jandor ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki, jim kadan da tattaunawarsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Legas: Tsohon dan takarar gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Galadima
Buba Galadima ya zargi APC da kwacen mulki Hoto: Comr Ahmad/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Galadima ya bayyana kafar Arise News cewa APC ce ta shiga, ta fita, har ta samu damar kwace mulkin gwamnatin jihar Legas daga hannun Jandor.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jandor, wanda ya zo matsayi na uku a zaɓen, inda ya samu ƙuri’u 62,449, yayin da gwamna mai ci, Babajide Sanwo-Olu, ya lashe zaɓen da kuri'u 762,134.

Duk da ikirarin, hukumar INEC ta sanara da cewa jam'iyyar PDP ta kare ne bayan APC da LP a zaben gwamnan jihar Legas da aka shirya a 2023.

2027: Jagoran NNPP ya yi bayanin shirin APC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Galadima ya bayyana cewa komawar Jandor zuwa APC wani yunkuri ne na jam’iyya mai mulki don tarwatsa jam’iyyun adawa.

Ya yi imanin cewa irin waɗannan sauya sheƙa na kawo cikas ga jam’iyyun adawa wajen taka rawar da ya kamata a gabanin zaɓen 2027.

Buba Galadaima
Jigon APC ya zargi 'yan adawa da rashin alkibla Hoto: Buba Galadima
Asali: UGC

Buba Galadima ya ce:

“Kun ga abin da Jandor ya aikata yanzu. Ku duba irin goyon bayan da mutanen Legas suka ba shi. A gaskiya, zan ce shi ne ya lashe zaɓen, sai dai kawai aka karɓe masa.

Kara karanta wannan

'Dan Sule Lamido ya bi sahun mahaifinsa, ya fadi kuskuren ƴan Najeriya a zaben 2023

“Amma yau, ku dubi abin da ya aikata; kawai ya juya baya ya koma APC.”

Buba Galadima ya soki 'yan adawa

Injiniya Buba Galadima ya nuna takaicinsa kan yadda ‘yan adawa ke biye wa son zuciya maimakon su tsaya tsayin daka wajen gudanar da siyasar akida.

Ya bayyana cewa:

“Yaya za mu gudanar da siyasar adawa? Dole ne mu yi siyasar adawa bisa akida. Ko da kai kaɗai ne, ka tsaya kan akidarka, ba bisa son abinci ba.”

Sai dai a bayanin da ya yi kafin sauya shekar, Jandor ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya koma APC shi ne ganin yadda jam’iyyar take da ƙarfin lashe zaɓe.

Ya kara da nanata cewa baya ga wannan, shi dan kishin kasa ne da ke da muradin ya ga ci gaban jihar Legas, ba a kashin kansa ba.

Buba Galadima ya yi zancen hadakar adawa

A baya, kun samu labarin cewa Jigon NNPP, Buba Galadima, ya yi tsokaci kan batun haɗakar jam’iyyun adawa a Najeriya domin a kawar da gwamnatin Bola Tinubu a a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Mene ake kitsawa?: Barau ya gana da Baffa Bichi da tsohon kwamishinan Abba

Buba ya ce za su iya yin haɗaka ne kawai da masu irin akidarsu, wato masu kishin talakawa da ba za su bari a ci gaba da wawure dukiyar al’umma da jefa su cikin matsi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel