2027: APC na Shirin ba Tinubu, Ganduje da Wasu 'Yan Majalisu Tikitin Tazarce

2027: APC na Shirin ba Tinubu, Ganduje da Wasu 'Yan Majalisu Tikitin Tazarce

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta fara shiri da gaske domin tunkarar babban zaben 2027 ba tare da ta fuskanci matsalolin cikin gida ba
  • Rahotanni sun bankado wasu daga cikin shirye-shiryen da ake yi, inda ake sa ran tabbatar da cewa Bola Tinubu ya samu tikitin tazarce
  • Yanzu haka, an kwadaitar da gwamnoni kan cewa za su iya yanke hukunci a kan dan majalisar dokokin da zai tsaya takara a jihohinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Yayin da siyasa ke kara zafi gabanin 2027, akwai alamun cewa shugaba Bola Tinubu da yawancin ‘yan majalisar tarayya da ke kan tutar APC za su samu tikitin tazarce.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki, wanda manyan jiga-jigan APC suka amince da shi, yunkuri ne na tabbatar da ikon Tinubu a kan tsare-tsaren jam’iyyar.

Kara karanta wannan

"Ba ka yi mana adalci ba," NLC ta yi raddi ga Obasanjo kan mafi karancin albashin N70,000

Tinubu
APC na shirin ba da tikitin tazarce Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Afolabi Henry Adedapo
Asali: Facebook

A labarin da ya kebantaga jaridar Leadership, an ruwaito cewa an bullo da batun bayar da tikitin tazarce ne domin gujewa rikicin shari’a da fusatattun 'yan jam'iyya kan ya kawo cikas da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ‘yan majalisa na komawa APC

Majiyar ta kara da cewa wannan shiri na bayar da tikitin takara kai tsaye yana daya daga cikin manyan dalilan da suka sa wasu manyan ‘yan majalisar adawa suka sauya sheka zuwa APC.

Haka kuma an gano cewa jam’iyyar na bai wa biyayya ga APC muhimmanci, duba da yadda zaben fitar da gwani mai zafi ke haddasa rikici da rabuwar kai a cikin jam’iyya.

Tinubu
Shugaban kasa na kokarin saita jam'iyyar a kan hanya kafin zaben 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shirin bayar da tikitin tazarce na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa ke kokarin hadewa domin kifar da Bola Tinubu a 2027.

A halin yanzu, ganawar da wasu jiga-jigan APC da suka fusata ke yi da manyan ‘yan adawa na kara bayyana yiwuwar ficewarsu zuwa SDP, karkashin jagorancin Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

Muhimman batutuwan da ke gaban APC

Sai dai wata majiya mai karfi da ta halarci taron kwamitin zartarwa na APC a Abuja ta ce an tattauna yiwuwar gudanar da taron da zai tabbatar da ci gaba da rike tsarin shugabanci na APC.

Majaiyar ta ce wannan zai hada daga matakin kasa, jiha, kananan hukumomi har zuwa mazabu, wanda ke nufin Abdullahi Umar Ganduje zai iya ci gaba da zama shugaban APC.

Ta ce duk da cewa wasu gwamnonin APC ba su gamsu da shirin ba, an tanadi hanyoyin da za su basu damar yanke hukunci kan wanda zai tsaya takara a majalisun jiha.

Jiga-jigan jam'iyyar APC za su sauya sheka

Majiyar ta kara da cewa shugaban kasa ya samu rahotannin tsaro da ke nuna cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka fusata suna shirin ficewa zuwa wasu jam’iyyun siyasa.

A cewarta:

“Amma dabararsu ita ce fara haddasa rikici a cikin APC idan aka gudanar da sabon taron jam’iyya don zaben shugabanni. Don hana haka, Shugaban Kasa ya yanke shawarar kada a gudanar da sabon taron jam’iyya ko babban taron kasa kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

“Ya fi mayar da hankali kan tabbatar da kwanciyar hankali a jam’iyya da gujewa rigingimun shari’a kafin zabe, wanda zai iya haifar da tsaiko.

'Dan APC ya hango wa Tinubu nasara

A baya, mun wallafa cewa jigo a jam’iyyar APC, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce babu wani haɗin gwiwar ‘yan adawa da zai iya hana Bola Ahmed Tinubu cin zabe a shekarar 2027.

Oyintiloye ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ya ce Tinubu yana da ƙwarewar siyasa da zai shi damar sake samun nasara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel