Majalisa Ta Jero Zunuban Gwamna, an Fadi Lokacin da Ake Hasashen Zai Rasa Kujerarsa

Majalisa Ta Jero Zunuban Gwamna, an Fadi Lokacin da Ake Hasashen Zai Rasa Kujerarsa

  • Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta aikawa Gwamna Fubara da mataimakiyarsa wasikar zargin saba doka, wanda zai iya janyo tsigewa
  • Wasikar na dauke da zargin kashe kudin gwamnati ba bisa ka'ida ba da hana majalisar yin aikinta yadda kundin tsarin mulki ya tanada
  • An ba Fubara da Odu kwanaki 14 don su maida martani, yayin da lauyoyi ke bukatar majalisar ta bi doka yadda ya kamata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers ka iya rasa kujerarsa ta gwamna kafin tsakiyar watan Yulin 2025 kan zarge-zargen da ake yi masa.

Wannan ya biyo bayan gabatar da zarge-zarge da wasikar saba doka da dama da majalisar jihar ke yi wa Gwamna Fubara da ka iya jawo masa matsala.

Gwamna ya shiga matsala yayin da ake ci gaba da shirin tsige shi
Majalisa ta gabatar da wasika mai dauke da saba doka da ake zargin Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Twitter

Majalisa ta rubuto zunuban Gwamna Fubara

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki matakin farko na tsige gwamna Fubara, ta jero tuhume tuhume

Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa Majalisar Dokoki ta jihar ta aikawa Fubara da mataimakiyarsa wasikar zargin aikata laifuka, don fara shirin tsige su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai wasu shawarwari na barin mataimakiyar gwamnati ko kuma nadin wani wanda ba ruwansa da rikicin siyasa ya rike jihar a matsayin mafita.

A bisa tsarin kundin mulki, ana iya tsige gwamna ko mataimaki cikin kwanaki 120, Fubara na da saura kwanaki 111 kafin a tsige shi.

Wasikar zargin Fubara ta fito daga shugaban Majalisa, Martin Amaewhule, sai dai kwamishinan yada labarai ya ce gwamnati ba ta karbi wasikar ba.

Wasikar da 'yan majalisa 26 suka sa hannu ranar 14 ga Maris, 2025, ta danganta zargin da sashe na 188 na kundin tsarin mulki.

Wasikar ta ce:

“Mu, 'yan majalisar dokokin jihar Rivers, muna mika maka wasikar zargin babban laifi da ka aikata a ofis.”
Majalisa na zargin Gwamna da saba doka
Majalisar jihar Rivers ta gabatar da zarge-zarge kan Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Fubara

Zargin sun hada da kashe kudin jama'a ba bisa doka ba da hana majalisa ta yi aikinta yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

Sauran laifukan sun hada da nada mukamai ba tare da tantancewa ba da kuma hana albashin majalisa da na sakataren majalisar.

Majalisa ta ce hakan ya saba wa sashen 121(3) na kundin tsarin mulki da sauran dokokin da ke aiki a Najeriya, cewar Punch.

Don haka, Majalisar ta ce Gwamna Fubara bai nuna kwarewa da shirin shugabanci bisa tsarin mulki da rantsuwar da ya dauka ba.

An mika irin wannan wasikar ga mataimakiyar gwamna, Prof. Ngozi Odu, inda aka zarge ta da taimakawa Fubara wajen kin mika kasafin kudin 2024.

Wasikar ta kara da cewa ta halarci taron majalisar zartarwa inda aka amince da cire kudi ba tare da dokar kasafi ba.

Majalisa ta baiwa Fubara da mataimakiyarsa kwana 14 don su mayar da martani kan zarge-zargen da aka yi masu.

Wike ya sake dura kan Gwamna Fubara

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce gwamna Siminalayi Fubara ya fadi siyasa kuma karin matsaloli za su mamaye shi.

Wike ya zargi Fubara da yawo da mutanen da suka nemi zama gwamna, yana cewa ba su da niyyar alheri ga jihar Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel