Filato: Kakakin Majalisar Dokoki na Tsaka Mai Wuya, APC Ta Buƙaci Ya Yi Murabus

Filato: Kakakin Majalisar Dokoki na Tsaka Mai Wuya, APC Ta Buƙaci Ya Yi Murabus

  • Shugabannin jam'iyyar APC sun fara huro wuta kan shugabancin Majalisar Dokokin Jihar Filato bayan an gama rikice-rikice
  • Jam'iyyar APC ta bukaci mambobinta su tsige kakakin Majalisar na yanzu watau Rt. Hon. Gabriel Dewan saboda su ne masu rinjaye
  • Shugaban APC na jihar Filato ya ce babu adalci a ce ɗan ƳPP ne ke jagorantar Majalisar duk da APC ke da mambobi 22 a cikin 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - APC da shugabanninta a Filato sun fara matsawa ‘yan majalisar jam'iyyar guda 22 don su tsige Kakakin Majalisar Dokoki, Hon. Gabriel Dewan.

APC ta fara matsin lamba ga mambobinta da ke Majalisar Dokokin Filato domin su sauke kakaki, wanda shi kaɗai ne ɗan jam’iyyar YPP.

Majalisar Dokokin Filato.
Jam'iyyar APC ta huro wuta a canza kakakin Majalisar Dokokin Filato Hoto: @PHofassembly
Asali: Twitter

Tribune Online ta tattaro cewa APC ta fara wannan yunkuri ne domin karɓe shugabanci a Majalisar Dokokin Filato, inda take da mafi rinjayen mambobi.

Kara karanta wannan

A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda APC ta zama mafi rinjaye a Majalisa

Idan ba ku manta ba Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen ‘yan majalisar PDP guda 22 a 2023, bisa hujjar cewa jam’iyyar ba ta da tsarin shugabanci da zai ba ta damar tsayar da ‘yan takara.

Wannan ya bai wa ‘yan takarar APC da suka zo na biyu a zaɓen zama zababbun ƴan Majalisar dokokin Filato.

Amma duk da haka, Gabriel Dewan na YPP ne ya ci gaba da zama Kakakin Majalisa bayan kotu ta kori ‘yan PDP.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin APC da wasu masu ruwa da tsaki a jihar na matsin lamba ga ‘yan majalisar don su bukaci Dewan ya yi murabus, ko kuma su cire shi.

APC ta yi zargin rashin adalci a Majalisa

Shugaban APC a Filato, Rufus Bature, ya ce rashin naɗa Kakakin Majalisa daga APC ba adalci ba ne, la’akari da cewa jam’iyyar ke da rinjayen mambobi 22 daga cikin 24.

Kara karanta wannan

2027: Jigon APC ya yi hangen nesa, ya hango abin da zai hana Tinubu yin tazarce

"A tsarin dimokuradiyya, mafi rinjaye ne ke yanke hukunci. Idan APC ta na da ‘yan majalisa 22, LP na da 1, YPP kuma na da 1, to ya zama abin mamaki a ce ɗan YPP ne ke jagorantar majalisa, dole ne a samu canji,” in ji Bature.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ba ta nufin haddasa tashin hankali, amma dole a yi abin da ya dace bisa tsarin doka.

Majalisar Dokoki ta yi martani

A nata bangaren, Majalisar Dokokin Filato ta tabbatar da cewa ana kan tattaunawa tsakanin APC da sauran jam'iyyu domin gyara shugabancinta.

Mai magana da yawun Majalisa, Hon. Matthew Kwarpo, ya ce:

"Shugaban APC ya bukaci a canza shugabancin majalisa saboda APC ke da mafi rinjaye. Amma muna son mu tabbatar da cewa muna ƙoƙarin yin wannan canji cikin lumana, ba tare da tada hankali ba.”

Ya kuma bayyana cewa Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya bukaci a kwantar da hankula don kaucewa rikicin siyasa kamar wanda ke faruwa a wasu jihohi irin su Ribas.

Kara karanta wannan

"Dama ƙarfa karfa aka mana a 2023," Sanata Tambuwal ya hango faɗuwar Tinubu a 2027

Gwamna Mutfwang.
Jam'iyyar APC ta bazo wuta kan shugabancin Majalisar Dokokin Filato Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

APC ta samu rinjaye a Majalisar Edo

A wani labarin, kun ji cewa APC mai mulki ta jam'iyya mafi rinjaye a Majalisar dokokin jihar Edo da mambobi hudu suka sauya sheƙa.

Ƴan Majalisar na LP da PDP sun tabbatar da komawa APC ne yayin da suka kai ziyara sakatariyar jam'iyyar da ke Birnin Benin da safiyar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel