'Yan Bangar Siyasa Sun Kashe Shugaban Matasa, Sun Ƙone Gidaje 9 a Sabon Farmaki

'Yan Bangar Siyasa Sun Kashe Shugaban Matasa, Sun Ƙone Gidaje 9 a Sabon Farmaki

  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta tabbatar da kisan Chigozie Nwoke, wanda aka ayyana a matsayin zakaran zaben matasa a Janairu
  • An kashe jagoran matasan ne a ranar 15 ga Maris da misalin karfe 9:00 na dare, inda aka raunata ‘yan uwansa hudu, aka kona gidaje tara
  • ‘Yan sanda na zargin wata kungiya da wani Chinaza Nwachukwu ke jagoranta da kai harin, yayin da aka fara farautar wadanda suka tsere

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Rundunar 'yan sandan Imo ta tabbatar da kisan Chigozie Nwoke, bayan an bayyana shi a matsayin zakaran zaben matasa da aka gudanar ranar 3 ga Janairu, 2025.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, Henry Okoye, ya bayyana cewa kisan ya faru ne a ranar 15 ga Maris, da misalin karfe 9:00 na dare, inda aka raunata ‘yan uwansa hudu.

Kara karanta wannan

Hatsabiban 'yan bindiga 18 da aka kashe a 2025 da tasirin hakan ga tsaron Arewa

Rundunar 'yan sanda ta yi magana da aka kashe shugaban matasa da kone gidaje a Imo
Rikicin siyasa ya jawo an kashe shugaban matasa a Imo, an kone gidaje tara. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

An kashe jagoran matasa a jihar Imo

Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddamar da ta biyo bayan sakamakon zaben matasan da aka yi a watan Janairu, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan sanda sun ce wata kungiya da ake zargin wani matashi, Chinaza Nwachukwu ke jagoranta ce ta kai harin, inda suka kona gidaje tara a yankin.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Aboki Danjuma, ya yi tir da kisan, tare da ziyarar yankin domin duba barnar da aka yi.

CP Aboki Danjuma ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da wadanda suka rasa gidajensu, yana mai tabbatar musu da cewa za a yi bincike don tabbatar da adalci.

Rikicin siyasar ya jawo an kona gida 9

Sanarwar Henry Okoye ta ce:

"Harin da aka kai a ranar 15 ga Maris, 2025, da misalin karfe 9:00 na dare, ya jikkata ‘yan uwansa hudu tare da kona gidaje tara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

"Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga zaben matasa da aka gudanar a ranar 3 ga Janairu, 2025, bayan an ayyana Nwoke a matsayin mai nasara."
"Ana zargin wata kungiya da wani Chinaza Nwachukwu ke jagoranta ce ta kai harin, amma har yanzu ba a kama dukkanin 'yan kungiyar ba."

Sanarwar ta ce kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar ta kama mutane hudu da ake zargi da hannu a harin, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke wadanda suka tsere.

'Yan sanda sun gargadi mazauna Imo

Rundunar 'yan sanda ta magantu kan rikicin siyasa da ya barke a jihar Imo
Imo: An kashe shugaban matasa da kone gidaje 9 yayin da rikicin siyasa ya barke. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sn ajiye gawar mamacin a dakin ajiyar gawa, yayin da wadanda suka jikkata ke samun kulawa a asibiti.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa an maido da zaman lafiya a yankin, tare da daukar matakan tsaro domin hana sake afkuwar irin haka.

Ya bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da bin doka da oda, yana mai jan hankalin matasa kan guje wa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Kogi: Rikici ya tsananta a SDP kwanaki da komawar El Rufai, jam'iyyar ta dare 2

CP Danjuma ya shawarci shugabannin al’umma da su rungumi hanyoyin sulhu wajen magance sabani don gujewa rikici a gaba.

Ya jaddada kudirin ‘yan sanda na kare lafiyar al’ummar jihar da tabbatar da doka da oda.

'Yan bindiga sun kashe kansila a Ebonyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe kansila da shugaban matasa a kauyen Isu, ƙaramar hukumar Onicha da ke jihar Ebonyi.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tare 'yan siyasar biyu, suka bude masu wuta sai da suka tabbatar sun mutu, sannan suka gudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng