Mutum ya mike daga dakin ajiye gawa bayan an bayyana mutuwarsa

Mutum ya mike daga dakin ajiye gawa bayan an bayyana mutuwarsa

- Wani mutum da ya farfado bayan ajiye a dakin gawa ana shirin yi masa sutura

- Mutumin Kiplangat Kigen mai shekara 32 ya fadi a gidansa kuma an garzaya da shi asibiti kuma aka yi tsammanin ya mutu a ranar Talata

- Hukumomin asibitin suna ci gaba da binciken dalili kai shi dakin adana gawarwaki bayan yana numfashi

Wani mai fama da matsananciyar jinya, wanda ya fadi a gidansa da ke Kenya kuma aka garzaya da shi asibiti, ya bawa masu kula da dakin ajiyar gawa mamaki bayan da ya farfado lokacin da ake shirin yi masa sutura.

Peter Kigen, mai shekara 32, an yi tsammanin ya mutu a ranar Talata kuma ma'aikatan asibitin Kapkatet, a yankin Kericho suka maida shi dakin gawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mutum ya mike daga dakin ajiye gawa bayan an bayyana mutuwar sa
Mutum ya mike daga dakin ajiye gawa bayan an bayyana mutuwar sa. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Wani mai kula da dakin adana gawar ya ce ya gano mutumin ya na numfashi lokacin da ya taba jikin sa.

Mai kula da dakin ne ya mika rahoton gaggawa ga jami'an asibitin aka kuma maida shi sashen bada kulawa ta musamman don ci gaba da ceton rayuwarsa.

Wani ma'aikacin asibitin, Gilbert Cheruiyot ya bayyana a ranar Laraba cewa wani mutum mai suna Kiplangat Kigen, mai shekara 32, ya farfado.

KU KARANTA: Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara

Cheruiyot an maida shi sashen kula da masu kowace irin larura kuma yana samun sauki.

Ya ce ana ci gaba da binkice don gano dalilin kai shi dakin gawa duk da cewa da ransa.

"Muna so musan menene hakikar abin da ya faru har ya sa aka bayyana wani ya mutu bayan ya na raye. Yanzu muna bincike kuma za mu bada gamsashen rahoto," a cewar Cheruiyot.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164