Legas: Tsohon Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

Legas: Tsohon Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Legas, Abdul'azeez Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sauga sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC
  • Kafin sauya sheƙarsa, Jandor ya gana da shugaba Bola Tinubu a Abuja don tattauna shawarar da ya yanke na komawa jam’iyyar APC a Legas
  • A kwanakin baya tsohon ɗan takarar gwamnan na PDP ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar bayan ya zargi shugabanninta da yi masa zagon ƙasa
  • Tun da farko Jandor jigo ne a jam'iyyar APC, sai dai ya fice ya koma PDP inda ya samu tikitin yin takarar gwamna a kakar zaben shekarar 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Legas na PDP, Dr. Abdul-Azeez Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2027: Jigon APC ya yi hangen nesa, ya hango abin da zai hana Tinubu yin tazarce

Abdul-Azeez Olajide Adeniran ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC ne bayan ya yi murabus daga PDP mai adawa a jihar.

Jandor ya koma APC
Abdul'azeez Adeniran ya koma jam'iyyar APC Hoto: @OfficialJandor
Asali: Twitter

Jandor ya koma APC bayan ficewa daga PDP

Tashar TVCNews ta rahoto cewa tsohon ɗan takarar gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin, 17 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jandor a yayin ganawar ya yi bayani kan tafiyarsa ta siyasa bayan da ya yi murabus daga jam’iyyar PDP.

Dr. Abdul'azeez Olajide Adediran shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas a babban zaɓen 2023 da ya gabata.

Komawarsa jam’iyyar APC na zuwa ne bayan zarge-zargen da ya yi wa wasu daga cikin ƙusoshin PDP kan cin dunduniyarta a zaɓen 2023.

Jandor ya gana da Bola Tinubu a Abuja

Bayan murabus ɗinsa daga jam’iyyar adawa, Adediran, wanda tsohon mamba ne na jam’iyya mai mulki a jihar, ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a Abuja don sanar da shi kudirinsa na komawa APC.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan: Tsohon shugaban majalisa ya fayyace gaskiyar shirin barin APC zuwa SDP

Hadimin Jandor, Gbenga Ogunleye, ya tabbatar da cewa ɗan siyasar na jihar Legas ya gana da shugaban kasa a sirrance a ranar Litinin, 10 ga watan Maris, a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Daga jam'iyyar APC zuwa PDP

Kafin ya koma PDP a watan Janairu 2022, Jandor ya kasance jigo a jam’iyyar APC, inda ya jagoranci ƙungiyar Lagos4Lagos Movement.

Ƙungiyar dai tana fafutukar ganin an samu adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar APC.

An riƙa kallon sauya sheƙarsa zuwa PDP a wancan lokacin a matsayin wani babban lamari a siyasar Legas, daga karshe ya samu damar lashe tikitin takarar gwamna a zaɓen fidda gwani.

Ahmad Lawan ya musanta shirin ficewa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya musanta batun cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyana rahotannin da ke cewa yana shirin komawa jam'iyyar SDP a matsayin marasa tushe ballantana makama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel