El Rufa'i Ya Fadi Matsayarsa kan Takara da Tinubu a Zaben 2027
- Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ba shi da tabbacin ko zai tsaya takara a 2027, ya bar wa jam’iyyar SDP da mutane zabi
- Ya bayyana cewa a baya ma, mutane suka roƙi Muhammadu Buhari har ya umarce shi da tsayawa takarar gwamna
- Tsohon gwamnan ya fayyace cewa kalamansa na “babu dattijo a Arewa” sun shafi ‘yan siyasa, ba dattijai na gaske ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya ce ba zai iya tabbatar da ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a 2027 ba.
Hakan na zuwa ne bayan ya sauya sheka daga APC zuwa SDP a makon da ya wuce, ya kasance cikin 'yan adawa.

Asali: Facebook
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, ya ce ba shi da ikon yanke wa kansa hukunci kan takara, domin hakan ya rage wa jam’iyya da al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi karin haske kan kalamansa na shekarar 2022 da suka ce “babu dattijo a Arewa,” ya ce batunsa ya shafi ‘yan siyasa da ke sayar da kai, ba dattawan kirki ba.
El-Rufa’i bai da tabbacin takara a 2027
A hirar da ya yi, El-Rufa’i ya ce bai san ko zai tsaya takara a 2027 ba, domin hakan mataki ne da jama'a da jam'iyya za su dauka.
"Ban sani ba. Ai ba ni ne zan ce zan yi takara ba. Jam'iyya ce da mutane za su kira ka su ce ka tsaya takarar wannan muƙami ko wancan,"
Ya ƙara da cewa ko takarar da ya tsaya ta gwamnan Kaduna a 2015, mutane ne suka je suka roƙi Muhammadu Buhari har ya umarce shi da tsayawa takara.

Asali: Twitter
A cewarsa:
"Mutane ne suka je suka samu Buhari suka gamsar da shi, shi kuma ya kira ni ya ce ka je ka yi takara, kuma ni ban ma so na yi takarar ba domin ban iya ba,"
El-Rufa’i ya fayyace maganar dattijo a Arewa
A shekarar 2022, El-Rufa’i ya ce babu dattijon Arewa yayin da yake mayar da martani kan wasu jiga-jigan yankin da ya zarga da kokarin hana Bola Ahmed Tinubu takara.
Sai dai daga baya wasu sun zargi El-Rufa’i da cewa kalamansa kuskure ne, duba da yadda yake fadin cewa an masa bazata a sabuwar gwamnati.
Lokacin da aka ta tambaye shi ko yana da-na-sanin furucinsa na cewa babu dattijo a Arewa, sai ya ce:
"A’a, ba cewa na yi babu wani dattijo a Arewa ba. Ni na san mutanen da ake magana a kai. Ba dattijai ba ne, ‘yan siyasa ne.
"Kuma kuɗi suke karɓa daga wurin wannan ɗan takara ko wannan jam’iyya. Ba Allah ne a gabansu ba, ba kuma Arewa ba."
El-Rufa'i na fatan Atiku ya shiga SDP
A wani rahoton, kun ji cewa Nasir El-Rufa'i ya yi fatan haduwa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a SDP.
Tsohon gwamnan ya ce haduwa da Atiku Abubakar da Peter Obi zai kara karfin 'yan adawa wajen tunkarar gwamnatin Bola Tinubu a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng