Matsalar Obasanjo da Atiku: Kalaman El Rufai Sun ba da Mamaki kan Rigimarsu a Baya
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce Olusegun Obasanjo ya fi gaskiya a rikicinsa da Atiku Abubakar
- El-Rufai ya ce ba siyasa ba ce ta haifar da goyon bayansa ga Obasanjo, ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da Atiku
- Tsohon gwamnan ya ce ya goyi bayan Bola Tinubu saboda dalilai na addini da yarjejeniyar siyasa kuma bai yi nadama ba
- Wannan na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan El-Rufai ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa SDP mai adawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ya yi magana kan rigimar Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar.
El-Rufai ya ce a lokacin rikicin da ya shiga tsakanin Obasanjo da Atiku, ya fi ganin tsohon shugaban yana kan gaskiya.

Asali: Twitter
Martanin El-Rufai kan jita-jitar sabani da Atiku
El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa bayan komawarsa jam’iyyar SDP daga APC a farkon wannan mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya ce ya yi aiki da Atiku cikin gaskiya inda ya tabbatar da cewa ya ji dadin aiki da shi matuƙa.
Ya ce:
"Na yi aiki da Atiku kuma na ji daɗinsa, amma siyasa ba ta haɗa mu ba, aiki ne ya haɗa mu, kuma na faɗa masa gaskiya."
El-Rufa’i ya musanta cewa yana da sabani da Atiku, yana cewa mutane ne kawai ke ta surutu, amma babu wata matsala tsakaninsu.
Ya ce mutane ne kawai ke ta yada jita-jitar inda ya ce da ace ya yi masa butulci da ba za su kasance da shi ba.
Ya ce:
"Mutane suna cewa na butulce wa Atiku, amma lokacin matsalarsa da Obasanjo, mun bincika, muka ga Obasanjo ne ke da gaskiya."
"A yanzu muna tare da Atiku, idan ni mai butulci ne, da ba za mu kasance tare ba, ya san gaskiya."

Asali: Facebook
El-Rufai ya magantu kan goyon bayan Tinubu
Game da goyon bayansa ga Tinubu, El-Rufa’i ya ce malamai daga Kudu maso Yamma sun roƙe shi ya taimaka a tabbatar da adalci ga Musulmi.
Ya ce dalili na biyu shi ne akwai yarjejeniyar cewa mulki zai koma Kudanci, kuma mutanen Arewa ba su saba alkawari.
Kan batun dattawan Arewa, ya ce:
"Ba cewa na yi babu dattijo ba, wadanda ke magana ba dattijai ba ne, ‘yan siyasa ne."
"Idan suna da gaskiya, ya kamata su fito su ce mulki ya koma Kudu bayan wa’adin Buhari."
Ana zargin ministoci 10 za su koma SDP
Kun ji cewa wasu rahotanni sun nuna alamu masu ƙarfi cewa guguwar sauya sheka na dab da ƙara turnuƙe APC bayan ficewar Nasiru El-Rufai, wanda ya koma SDP.

Kara karanta wannan
'Ku biyo ni TikTok': El-Rufai ya bude shafinsa, ya tara dubban mabiya cikin sa'o'i 24
An ce tsofaffin ministoci 10 da suka yi aiki a Gwamnatin Muhammadu Buhari da manyan jiga-jigai na shirin bin sawun Malam El-Rufai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng