Tsofaffin Ministocin Buhari 10 da Manyan Kusoshi na Shirin Bin El Rufai zuwa SDP
- Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa guguwar sauya sheka na dab da ƙara turnuƙe APC bayan ficewar Nasiru El-Rufai, wanda ya koma SDP
- Rahotanni su na zargin tsofaffin ministoci 10 da suka yi aiki da Muhammadu Buhari da manyan jiga-jigai na shirin bin sawun El-Rufai
- Daga cikin waɗanda ake sa ran za su tsallaka zuwa SDP har da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da Abubakar Malami SAN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƙarin alamu masu ƙarfi na nuna cewa tsofaffin ministoci a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar SDP.
Wani tsohon sanata a Majalisa ta Tara, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa ƙalla ministoci 10 daga tsohuwar gwamnatin Buhari na shirin shiga SDP.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta tattaro cewa tsofaffin gwamnoni da jiga-jigan APC da dama na shirye-shiryen bin sawun Nasir El-Rufai zuwa SDP.

Kara karanta wannan
Bayan El Rufai ya yi fatan ya dawo SDP, alamu sun nuna Peter Obi na shirin canza jam'iyya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan kusoshin da ke hanyar shiga SDP
"Abin da suke jira kawai shi ne a kammala tsarin jagoranci na jam’iyyar a jihohinsu," in ji majiyar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa manyan magoya bayan Buhari da ke kan gaba a wannan ƙaura sun haɗa da:
- Abdullahi Adamu – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa
- Abubakar Malami – Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan shari'a.
- Ahmed Lawan – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa
El-Rufai ya fara yin gaba zuwa SDP
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauya sheƙa zuwa SDP a ranar Litinin, yana mai cewa manufofinsa da na APC sun yi hannun riga a yanzu.
"Abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka wuce sun tabbatar da cewa waɗanda ke rike da APC a yanzu ba su da niyyar gyara matsalolin jam’iyyar," in ji El-Rufai.
Shin Buhari ya amince da shirin?
El-Rufai ya bayyana cewa ya nemi amincewar Buhari kafin barin APC. Wannan kuwa ya ƙara janyo tururuwar ‘yan jam’iyyar APC, musamman na ɓangaren CPC zuwa SDP.
Buhari, El-Rufai, Malami, da Lawan sun kasance manyan jagororin CPC har zuwa hadewarta da jam'iyyun ACN, APGA, da nPDP don kafa APC a shekarar 2013.
Rahoton ya nuna cewa wannan ƙaura da ake yi daga APC zuwa SDP ba kawai tasgaro ne ga gwamnati mai ci ba, za ta iya zama gagarumin haɗin gwiwa na jiga-jigan ‘yan siyasa.
Shin hakan na da nasaba da zaɓen 2027?
Wani babban na hannun daman Malami ya tabbatar da shirin haɗin gwiwa, amma ya musanta cewa manufarsu ita ce hamɓarar da Tinubu a 2027.
"Ba lallai ne ya zama batun kawar da Tinubu ba, amma dai muna ganin akwai wnai zaɓi mafi kyau da ya fi dacewa da dimokraɗiyya don tafiyar da Najeriya," in ji shi.

Asali: UGC
Wata majiya mai tushe ta ce tsoffin gwamnoni irin su, Rotimi Amaechi (Rivers), Emeka Ihedioha (Imo), Liyel Imoke (Cross Rivers), Aminu Tambuwal (Sokoto), da Rauf Aregbesola (Osun) su na cikin waɗanda ke nazarin komawa SDP.
Har ila yau, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Shugaban APC, John Odigie-Oyegun, tsohon ƙaramin ministan Ilimi na Buhari, Emeka Nwajiuba, da sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, suma suna cikin wannan shiri.
SDP na ci gaba da tattaunawa da jiga-jigai
Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Lalong, wanda ya koma SDP tun 2022, ya tabbatar da cewa akwai muhimman tattaunawa da ‘yan siyasa ke yi a yanzu.
"Muna cikin tattaunawa da mutane daga sassa daban-daban, ciki har da tsoffin ministoci da sanatoci. Amma saboda muna cikin matakin tattaunawa, ba zan bayyana sunayensu ba a yanzu,"
- in ji Lalong.
Wani jigon APC da ya koma SDP tun bayan sauya shekar El-Rufai ya shaidawa Legit Hausa cewa da yawan matasan jam'iyya mai mulki na sha'awar wannan tafiya.
Usman Sa'ad ya ce lokaci alƙali amma alamu na nuna cewa ƴan adawa na dab da kawo ƙarshen mulkin APC a Najeriya.

Kara karanta wannan
Kalaman El Rufa'i sun tada ƙura, ƴan sanda sun yi magana kan zargin 'sace kwamishina'
"Malam na komawa SDP na bi shi, kuma abin farin cikin matasan da muke tare da su a APC sun nuna sha'awar shigowa wannan tafiya. Mutane sun gaji da wannan mulkin, muna bukatar mutane kamarsu El-Rufai," in ji shi.
MC Tagwaye ya bar APC zuwa SDP
A wani labarin, kun ji cewa shahararren mai barkwanci kuma dan siyasa, Obinna Simon wanda aka fi sani da MC Tagwaye, ya bar APC, ya bi El-Rufai zuwa APC.
MC Tagwaye wanda ya shahara bisa kwaikwayon maganar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce APC ta sauka daga manufofinta na asali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng