Ana Zargin El Rufai Zai Fice daga APC, Ɗansa Bashir Ya Nuna Jam'iyyar da Ya Koma

Ana Zargin El Rufai Zai Fice daga APC, Ɗansa Bashir Ya Nuna Jam'iyyar da Ya Koma

  • Ana zargin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana
  • Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan, ya wallafa hoton SDP a shafinsa na intanet, wanda ke nuna alamar jam'iyyar da El-Rufai ya koma
  • Wata majiya daga tsohuwar gwamnatin El-Rufai ta tabbatar da Malam zai sauya sheka zuwa SDP a yau, Litinin, 10 ga Maris 2025

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Da alama dai akwai kamshin gaskiya, a kan rahotannin da wasu kafafen labarai suke yadawa na cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fice daga APC.

Wadannan kafafen yada labarai, sun yi ikirarin cewa Mallam Nasir El-Rufai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP mai alamar doki.

Bashir ya nuna alamar jam'iyyar da mahaifinsa, Nasir El-Rufai ya koma
SDP, APC: Dan tsohon gwamnan Kaduna, Bashir ya nuna alamar da jam'iyyar da El-Rufai ya koma. Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

Ana tsakiyar yada wadannan rahotanni da ba a tabbatar da su a hukumance ba, sai kuma Legit Hausa ta ci karo da wallafar Bashir El-Rufai a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Nasir El Rufai ya fitar da sanarwar ficewa daga APC zuwa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir ya nuna jam'iyyar da El-Rufai ya koma

Kowa ya san Bashir El-Rufai, dana ne ga tsohon gwamnan na Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma mai yada manufofin mahaifinsa a soshiyal midiya.

Da misalin karfe 10:13 na safiyar Litinin, 10 ga Maris din 2025, Bashir El-Rufai ya wallafa hoton jam'iyyar SDP, ba tare da ya ce 'uffan' a kan hoton ba.

Sai dai, masu bibiyarsa, sun yi amanna da cewa Bashir ya fitar da alamar jam'iyyar da mahaifinsa, Nasir El-Rufai ya koma bayan ficewa daga APC.

Da wannan wallafar ta Bashir, mutane suka fara gaskata cewa, tsohon gwamnan na Kaduna ya watsar da APC da gaske, kuma ya koma layin jam'iyyarsu Shehu Gabam.

Rahoton ficewar El-Rufai daga jam'iyyar APC

El-Rufai ya ziyarci shugabannin jam'iyyar SDP
El-Rufai ya gana da shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam. Hoto: @IU_Wakilii
Asali: Twitter

Bugu da kari, bayan wallafa hoton jam'iyyar SDP, sai kuma aka ga Bashir ya raba wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar, da ya nuna cewa El-Rufai ya fice daga APC.

Kara karanta wannan

Nasir El Rufa'i ya sauya sheka, ya fita daga APC zuwa SDP

Rahoton ya nuna cewa, wani na hannun damar El-Rufai ya tabbatar da ficewar tsohon gwamnan Kaduna daga APC, bayan bullar wata wasika a kafafen sada zumunta.

Majiyar, wacce ta yi aiki a matsayin kwamishina a gwamnatin El-Rufai, ta shaida cewa El-Rufai zai sauya sheka zuwa SDP a yau Litinin.

"Eh, mun san cewa zai ajiye mukaminsa a APC a yau, Litinin, 10 ga Maris, 2025, sannan ya koma SDP. Wannan ne kawai muke jira,"

- Inji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa magoya bayan El-Rufai ba su yi mamakin bullar wasikar ba, domin sun rigaya sun san da batun ficewar tasa.

El-Rufai ya gana da shugaban SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon sanatan Katsina, Ahmad Babba Kaita, da Mustapha Inuwa sun gana da shugabannin SDP.

Shugaban jam’iyyar, Shehu Musa Gabam, wanda ya bayyana abin da tattaunawar ta mayar da hankali, ya ce SDP na shirin sake fasalin siyasar kasar tare da su El-Rufai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.