Ta Faru Ta Kare: Atiku Ya Yi Magana kan Barin PDP, Ya Fadi Shirinsa

Ta Faru Ta Kare: Atiku Ya Yi Magana kan Barin PDP, Ya Fadi Shirinsa

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya taɓo batun jita-jitar shirinsa na barin jam'iyyar PDP
  • Atiku ya bayyana rahotannin da ke cewa yana shirin barin PDP a matsayin ƙarya maras tushe ballantana kuma makama
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya nuna aniyarsa ta ganin an samu gagarumar haɗaka wacce za ta kawar da APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan barin jam'iyyyar.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar PDP.

Atiku ya musanta barin PDP
Atiku ya ce har yanzu shi mamba ne a jam'iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar a ranar Asabar, 8 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya musanta raɗe-raɗin barin PDP

Sanarwar ta bayyana rahotannin da ke cewa Atiku Abubakar na shirin barin PDP a matsayin tatsuniyar gizo da ƙoƙi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP na goyon takarar El Rufai, Peter Obi a 2027? An fede gaskiya

A cikin wannan ƴan kwanakin nan, akwai wasu rahotannin da ke cewa Atiku masu cewa na shirin barin PDP domin shiryawa zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A martanin da ya fitar, Atiku ya bayyana cewa yana ƙoƙarin haɗa gagarumar haɗaka ta jam'iyyun adawa, wacce za ta haɗa har da jam'iyyar PDP, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Mun lura da cewa wasu kafafen yaɗa labarai na yaɗa labaran da ba su da tushe kan cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar zai bar jam'iyyar PDP."
"Muna son mu fayyace cewa waɗannan labaran masu cewa Atiku zai koma wata jam'iyya soki burutsu ne kawai."
"Idan ba a manta ba dai Atiku ya sha kiran yin haɗakar jam'iyyun adawa kafin zaɓen 2027 da niyyar kawar da jam'iyyar APC wacce ta gaza domin kawo sauƙi ga ƴan Najeriya kan wuyar da take ba su."
"Atiku yana neman a samar da babbar haɗaka wacce za ta ƙunshi dukkanin jam'iyyun adawa, ciki har da PDP."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ganduje ya sa lokacin yin jana'izar PDP, ya yi gayyata

- Ofishin yaɗa labaran Atiku

Me Atiku ya ce kan barin PDP?

Atiku Abubakar ya bayyana iƙirarin da ke cewa yana shirin barin PDP a matsayin ƙarya wacce ba ta da tushe ballantana makama.

"Saboda haka ƙarya ce kawai a yi zargin cewa Waziri zai fice daga jam'iyyar PDP. Wannan zargin ya ci karo da manufar yin haɗaka wacce tsohon mataimakin shugaban ƙasan yake jagoranta tare da sauran manyan ƴan siyasa a ƙasar nan."
"Saboda haka, muna fayyace cewa har yanzu Atiku cikakken mamba ne na jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa."

- Ofishin yaɗa labaran Atiku

Magoya bayan Atiku sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƙungiyoyin da ke goyon bayan Atiku Abubakar a jihohin Arewa 19, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, suka karɓi ƙungiyoyin a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng