Da Gaske ne Atiku Ya Sauya Sheka, Zai Yi Takarar 2027 a SDP?

Da Gaske ne Atiku Ya Sauya Sheka, Zai Yi Takarar 2027 a SDP?

  • Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya karyata jita-jitar cewa tsohon dan takarar shugaban kasan ya sauya sheka
  • An fara yada jita jitar yayin da ake tsammanin tattaunawar hadewar Atiku da wasu ‘yan takarar shugaban kasa da suka buga a zaben 2023
  • Sai dai wani cikin hadiman dan siyasar ya kara jaddada cewa maganar sauya shekar, labarin na kanzon kurege ne da ke kokarin rudanar al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ana ta yada jita-jitar cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa SDP.

Wannan labari ya karade kafafen sada zumunta, inda wasu ke cewa hakan na iya shafar tattaunawar hadin gwiwa da wasu ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

"An yi rashin nasara sau 3," Shugaba a PDP ya ja kunne kan tsaida Atiku takara a 2027

Atiku
Atiku ya musanta sauya sheka zuwa SDP. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sai dai hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya karyata labarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin na zuwa ne yayin da ake tsammanin tattaunawa tsakanin Atiku da wasu ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, kamar Peter Obi na jam’iyyar LP.

Haka zalika ana hasashen cewa tattaunawar za ta hada da Rabiu Kwankwaso na NNPP, domin yiwuwar hada karfi a siyasa.

Yayin magana a kan labarin, hadimin na Atiku Abubakar ya ce ba gaskiya ba ne zancen, kuma an kirkire shi ne domin a yaudari jama’a.

Atiku bai bar PDP ba in ji Abdul Rasheeth

Mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a bangaren watsa labarai, Abdul Rasheeth ya musanta rade-radin cewa Atiku ya bar jam’iyyar PDP zuwa SDP.

Hadimin Atiku ya bayyana hakan ne domin karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023 ya fice a PDP zuwa SDP.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Shirin tattaunawa da wasu ‘yan siyasa

The Cable ta wallafa cewa jita jitar da ke yawo ta jawo mamaki kan dalilin da zai sa Atiku ya yanke wannan shawara, alhali kuwa ana tsammanin yin hadakar 'yan adawa.

Ana tsammanin hadakar ne tsakanin shi da tsofaffin ‘yan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

A cewar rahoton, ana tsammanin samar da hadin gwiwa tsakanin Atiku, Obi na jam’iyyar LP da kuma Kwankwaso na NNPP domin tunkarar zaben 2027 tare.

Atiku
Atiku da jagoran LP, Obi. Hoto: Mr. Peter Obi|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku bai shiga SDP ba – Rasheeth

Da yake mayar da martani kan batun, Abdul Rasheeth ya kara da cewa:

“Kada a yarda da wannan jita-jitar! Atiku Abubakar bai shiga jam’iyyar SDP ba, kuma ba zai shiga ba. Wannan jita-jita ce kawai da aka kirkira domin a rudanar da jama’a.”

Hadimin Atiku ya jaddada cewa labarin ba gaskiya ba ne, kuma wani yunkuri ne na wasu mutane da ke kokarin wargaza siyasar Atiku da makomarsa.

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Majalisa za ta yi sauye sauye a INEC

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta fara shirin sauye sauye ga hukumar INEC yayin da aka fara maganar zaben 2027.

Majalisar ta fara yunkurin kirkirar hukuma ta musamman domin cigaba da lura da rajista da lura da jam'iyyun siyasa da INEC ke yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng