2027: Gwamna Ya Halarci Lakcar Ramadan, Ya Taɓo Batun da ba a Yi Tsammani ba

2027: Gwamna Ya Halarci Lakcar Ramadan, Ya Taɓo Batun da ba a Yi Tsammani ba

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya halarci wurin lakcar da aka shirya saboda zuwan watan azumin Ramadan a fadar gwamnatinsa da ke Ibadan
  • Duk da ba a yi tsammanin zai tabo batun siyasa ba, Gwamna Makinde ya ce a watan Janairu, 2026 zai faɗi sunan wanda zai gaji kujerarsa a 2027
  • Gwamnan ya kuma buƙaci al'ummar musulmi su yi amfani da wannan lokaci mai albarka wajen yi wa jihar Oyo da ƙasa addu'ar zaman lafiya da ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da cewa zai bayyana wanda zai goyi bayan ya zama magajinsa a babban zaɓen 2027.

Injiniya Seyi Makinde ya tabbatarwa al'ummar jihar Oyo cewa zai sanar da sunan wanda yake so su zaɓa ya zama magajinsa a watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya yi gargadi kan siyasantar da tsaro bayan kalaman El-Rufa'i

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamna Makinde zai bayyana wanda zai gaji kejerarsa a watan Janairun 2026 Hoto: Seyi Maikinde
Asali: Facebook

Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi a wurin wa’azi da lakcar Ramadan na Omituntun karo na 11, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da wannan taro ne domin tunatar da musulmi falalar Ramadan a filin taro na gidan gwamnati da ke Ibadan.

Gwamna ya buƙaci musulmi su yi addu'a

Taron lakcar na bana an masa taken “Fa’idodin zama makwabci na gari: Bisa koyarwar addinin Musulunci."

Babban limamin Ogbomoland, Sheikh Yunus Teliat, ne ya gabatar da lakcar ta bana 2025/1446H.

Da yake jawabi cikin harshen Yarbanci, Makinde ya gode wa shugabannin da malaman addinin musulunci bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa.

Haka nan kuma Gwamna Seyi Makinde ya roƙe su da su ci gaba da yin addu’a don zaman lafiya da ci gaban jihar Oyo.

Ba a rufe shafin siyasa na ba" - Makinde

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kudin ciyarwa a Ramadan, ta fadi abin da za ta kashe

A cikin raha, gwamnan ya yi magana kan Abbas Oloko, wani shahararren ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa, yana mai cewa kada ya cire allon kamfen da ya manna a Isale Alfa.

"Ba a rufe shafin siyasa na ba. Don haka, don Allah, ka bar allon da ke Isale Alfa a nan. A watan Janairu 2026, mun san cewa za a fara harkokin siyasa. A lokacin, zan bayyana wanda zai gaji kujerar nan."

Gwamna ya aika saƙo ga musulmi

Makinde ya kuma ƙarfafa musulmi da su yi amfani da watan Ramadan don yaɗa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar jihar, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.

A ƙarshe, ya buƙaci musulmi su sanya jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya a cikin addu'o'insu a wannan wata mai albarka, rahoton Vanguard.

Wannan kalamai na Gwamna Seyi Makinde na zuwa ne yayin da musulmi a Najeriya suka fara ibadar azumin watan Ramadan bayan ganin wata a daren Juma'a.

Kara karanta wannan

'Abubuwan da ya kamata musulmi su dage da yi a watan azumin Ramadan'

Gwamna Makinde ya yi naɗe-naɗe a Oyo

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamma Seyi Makinde ya naɗa sababbin manyan sakatarori 45, karo na farko a tarihin jihar Oyo.

Mutum 16 daga cikin sababbin manyan sakatarorin da Gwamna Makinde ya nada za su yi aiki ne a ma'aikatun gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262