Kusa a APC Ya Kinkimo Aikin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje da Shekarau a Kano
- Jigo a jam'iyyar APC a Kano ya nuna damuwa kann rashin haɗin kan da ke tsakanin manyan ƴan siyasar jihar guda uku
- Abdulkarim Abdulsalam Zaura ya shirya aiki domin sasanta Rabiu Musa Kwakwaso, Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau
- Tsohon ɗan takarar sanatan na jam'iyyar APC ya bayyana cewa siyasar adawa da ake yi a Kano, ba ta da wani amfani ga jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jigon APC a Kano, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, da aka fi sani da AA Zaura, ya bayyana aniyarsa ta sasanta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje, da Ibrahim Shekarau.
AA Zaura ya ce sasantawa tsakanin shugabannin siyasar Kano zai canza yanayin siyasar jihar daga adawa zuwa ta cigaba.

Source: Facebook
Ana son sasanta Kwankwaso, Ganduje da Shekarau
Jigon na APC ya ce sasanta jiga-jigan ƴan siyasa zai bunƙasa ci gaban Kano, kamar yadda ake gani a Legas da wasu manyan jihohi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban Majalisa ya goyi bayan kudirin ƙirkiro jiha 1 a Arewa, an faɗi sunanta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
AA Zaura ya nuna damuwa kan yadda rabuwar kai tsakanin waɗannan manyan ƴan siyasa ke hana Kano ci gaba.
Ya jaddada cewa haɗa kan shugabannin uku shine mabuɗin bunƙasa ci gaban jihar.
"Siyasar adawa da ake yi a Kano a halin yanzu ba ta da wani amfani. A shirye nake na yi aiki don ganin cewa shugabannin siyasar mu guda uku, Kwankwaso, Ganduje, da Shekarau sun haɗa kai."
"Ya kamata a duba ci gaban Kano, ba muradin kowa da kowa ba. Idan hakan ta samu, Legas da wasu jihohi za su koyi darasi daga siyasar cigaban da za mu kafa a Kano."
- Abdulsalam Abdulkarim Zaura
An yi yunƙurin sasanta jiga-jigan siyasar Kano
A baya, an yi ƙoƙarin sasantawa tsakanin Ganduje, shugaban APC na ƙasa, da Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, amma ba a samu nasara ba saboda tsatstsauran bambancin siyasa da ke tsakaninsu.
Ƙoƙari na ƙarshe ya samu cikas ne lokacin da magoya bayan Kwankwaso suka goyi bayan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, domin ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban APC na ƙasa.
A wancan lokaci, Ganduje ya jaddada cewa shi uba ne ga duk wanda yake son shigowa jam’iyyar, kalmar da mutane da dama suka fassara a matsayin abin da ya ƙara dagula yunkurin sasantawar.
AA Zaura ba shi kaɗai ba ne ke fafutukar ganin an samu zaman lafiya a tsakanin jagororin siyasar Kano.
Wasu jiga-jigan APC, ciki har da mataimakin ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo, da babban ɗan siyasa, Baffa Babba Danagundi, suma sun yi irin wannan kira.
Kwankwaso, Ganduje, da Shekarau, dukkansu sun yi gwamna a Kano na tsawon wa’adi biyu, kuma kowannensu yana da ƙaƙƙarfan tasiri a matakin jiha da na ƙasa, duk da cewa suna cikin jam’iyyun siyasa daban-daban.
Ganduje ya taya Musulmai murnar shigowar Ramadan
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya al'ummar Musulmai murnar zuwan watan azumin Ramadan.
Ganduje ya buƙaci al'ummar Musulmai da su dage da addu'o'i tare da taimakon marasa galihu a cikin watan azumin Ramadan na bana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
