Kotun Koli Ta Jiƙawa Gwamna Aiki, Ta Tsige Shugabannin Kananan Hukumomi 23

Kotun Koli Ta Jiƙawa Gwamna Aiki, Ta Tsige Shugabannin Kananan Hukumomi 23

  • Kotun koli ta tsige shugabannin kananan hukumomin jihar Ribas, ta bayyana cewa zaɓen da aka gudanar ya saɓa wa kundin dokar zaɓe
  • A yau Juma'a, Alkalin kotun mai daraja ta ɗaya Najeriya, Mai Shari'a Jamilu Tukur ne ya yanke wannan hukuncin a ƙarar da APC ta shigar
  • Ya ce hukumar zaɓe ta jihar Ribas ta karya doka da ta tsallake wasu matakai yayin shiryawa da gudanar da zaɓen wanda hakan ya ka'ida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun Kolin Najeriya ta sauke dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ribas, waɗanda aka zaɓa a zaɓen ciyamomi da kansilolin da aka yi a watan Oktoba.

Kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta bayyana zaɓen ƙananan hukumomin Ribas da aka yi ranar 5 ga watan Oktoba 2024 a matsayin wanda ya saɓa doka.

Kara karanta wannan

Ana murnar Ramadan, an kama shugaban ƙaramar hukuma da zargin sata a Kano

Kotun koli.
Kotun koli ta soke zaben ciyamomi da kansilolin da aka yi a jihar Ribas Hoto: Supreme Court
Asali: Facebook

Mai shari'a Jamilu Tukur ne ya yanke wannan hukunci a ƙarar da aka shigar gabansa kan zaɓen da Hukuma ta shirya, Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaɓen kananan hukumomi a Ribas

Idan ba ku manta ba a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024 Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta jihar Ribas watau RSIEC ta gudanar da zaɓen ciyamomi da kansiloli.

Sakamakon zaɓen ya nuna cewa jam'iyyar APP wadda ke da goyon bayan Gwamna Fubara ta lashe kujerun ciyamomi 22 yayin da jam'iyyar AA ta ci kujera ɗaya.

Kotun koli ta rusa zaɓen jihar Ribas

Kotun Koli ta Najeriya ta bayyana zaben kananan hukumomi da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Rivers (RSIEC) ta gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024 a matsayin ba bisa ka’ida ba.

A hukuncin da Mai shari’a Jamilu Tukur ya yanke, kotun ƙolin ta ce an soke zaben ne saboda sabawa dokoki da kuma rashin bin ka’idojin gudanar da zabe.

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

Dalilin tsige shugabannin ƙananan hukumomi

Mai shari’a Jamilu ya ƙara da cewa Hukumar Zabe ta jihar Ribas ta aikata laifi da ta ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a bayan ta riga ta sanar da ranar zabe.

Kotun ta kuma yanke hukunci cewa an tsallake wasu matakai na shirye-shiryen gudanar da zaben, wanda hakan ya sabawa sashe na 150 na dokar zabe ta Najeriya.

Gwamna Fubara da Wike
Kotun koli ta ce an saɓa doka wajen gudanar da zaɓen kananan hukumomi a Rivers Hoto: Sir. Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Saboda haka, alkalin kotun kolin ya ayyana cewa dukkanin sakamakon zaben da aka gudanar sun zama marasa inganci a idon doka.

Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Ribas ce ta shigar ƙara a gaban kotun ƙoli tana ƙalubalantar zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar.

Kotun koli ta kori ƙarar Gwamna Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa kotun Koli ta yi watsi da karar da Gwamna Siminalayi Fubara ya shigar yana neman a tsige ‘yan majalisar dokoki guda 27.

Bayan haka kuma kwamitin alkalan kotun ƙarƙashin mai shari Uwani Abba Aji ya kuma ci tarar Gwamna Fubara kuɗi Naira miliyan 2.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262