"Tsintsiya Madaurinki Daya Mu ke," Gwamnan APC Ya Yi Watsi da Zargin El Rufa'i

"Tsintsiya Madaurinki Daya Mu ke," Gwamnan APC Ya Yi Watsi da Zargin El Rufa'i

  • Shugabannin APC sun musanta zargin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i na cewa jam'iyyar ta na fama da matsaloli da dama
  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce jam'iyyarsa a hade take, sannan ba ta da wasu manyan kalubale kamar yadda ake fada
  • Ya kara da cewa yanzu haka, gwamnatinsu ta APC ta na samun karin kudin shiga, wanda ya kara bata damar gudanar da manyan ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugabannin APC sun musanta zargin da ake yi cewa jam'iyyar mai mulki na gudanar da harkokinta ne a matsayin "shahararren mulkin mutum daya."

Akwai zage-zarge da dama daga mutane daban-daban, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya bayyana cewa jam'iyyar ta zama ta mutum daya kawai.

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

Uzodinma
An musanta baraka a APC Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya caccaki APC bisa watsi da ka'idojin jam'iyyar, kuma ya ce an kauce daga tsarin da aka dora ta a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma El-Rufa'i na zargin tabarbarewar jam'iyyar ce ta sa aka gaza gudanar da tarukan da ya kamata a ce an dade da gudanar da su.

Martanin shugabannin APC ga Nasir El-Rufai

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya shaida wa 'yan jarida cewa APC na ci gaba da kasancewa tsitsiniya madaurinki daya.

Ya kara da cewa kundin tsarin jam'iyyar yana da tsarin jagoranci wanda ke tabbatar da haɗin kai wajen yanke shawara.

Uzodimma ya ce:

"APC jam'iyya ce mai girma sosai da shugabanni a dukkan matakai. Ban san ma'anar hadin kai ba idan ana wakiltar yankunan siyasa guda shida," in ji Uzodimma.
"Jam'iyyar mu tana daya, mai karfi, mai maida hankali, kuma tana goyon bayan gwamnati. Dole mu yi murna da nasarorinmu."

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauke Ganduje a shugaban APC? Sakataren jam'iyya ya magantu

APC tana goyon bayan gwamnatin Tinubu

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya dage cewa jam'iyyar tana ba da cikakken goyon baya gagwamnatin tarayya, karkashin Bola Tinubu.

Jihar
Gwamnan Imo ya ce gwamnati ta kara samun kudin shiga Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Ya ce:

"Gwamnatin tana samun goyon baya sosai daga APC, kuma lokaci-lokaci, dole mu nuna cewa muna tare da gwamnati.
"Muna da tsarinmu na ciki don zaɓe da aiwatar da dimokuradiyya. Me yasa muke cin nasara a dukkanin zaben nan? Saboda mun nuna babban ƙarfin hali da girmamawa ga dimokuradiyya."

'APC tana samun kudin shiga' - Gwamna Uzodimma

Gwamnan jihar Imo ya bayyana cewa jam'iyyar ta kara inganta samun kudin shiga a yanzu, wanda ya bai wa jam'iyyar damar zuba jari a cikin ababen more rayuwa.

Ya kara da cewa jam'iyyarsa ta zama abin kishi da koyi ga sauran jam'iyyun adawa, sannan ta yi zarra a tsakanin takwarorinta da ke sassan Afrika.

El-Rufa'i ya soki shirin gwamnatin APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana ra'ayinsa game da wasu daga cikin manufofin gwamnatin tarayya, karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje sun kira taron kusoshin APC a Abuja

Ya bayyana cewa yana goyon bayan wasu daga cikin manufofin, amma ya nuna damuwarsa game da yadda ake aiwatar da su, wanda yake ganin cewa wannan ne zai lalata shirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.