Sanatan da Ya Koma APC Na Fuskantar Barazana daga Ƴan Mazabarsa, Sun Kai Shi Kotu

Sanatan da Ya Koma APC Na Fuskantar Barazana daga Ƴan Mazabarsa, Sun Kai Shi Kotu

  • Sanata Ned Nwoko ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, wanda ya sa aka bukaci kotu da ta ayyana kujerarsa a matsayin babu mai rike da ita
  • Wani dan PDP, Marvis Ossai, ya bukaci kotu ta umarci INEC ta gudanar da sabon zaɓe, tare da soke takardar shaidar cin zaɓen da aka ba Nwoko
  • A cewarsa, Nwoko yana wakiltar wata manufa daban da wacce aka zaɓe shi akanta, kuma hakan na iya ƙarfafa cin amanar jam’iyya a majalisa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An bukaci kotun tarayya da ke Abuja da ta ayyana kujerar Sanata Ned Nwoko (Delta ta Arewa) a matsayin babu mai rike da ita, bayan ya sauya sheka zuwa APC.

Marvis Ossai, ɗan PDP daga Delta ta Arewa, ya bukaci kotu da ta umarci INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi cikin kwanaki 60 bayan yanke hukunci.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

An yi karar Sanata Ned Nwoko bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
An nemi kotu ta ayyana kujerar Sanata Ned Nwoko a matsayin ba kowa a kanta bayan ya koma APC. Hoto: @GovUmarGandujee
Asali: Twitter

Dan mazaba ya maka sanatan Dalta a kotu

Baya ga Sanata Nwoko, hukumar INEC, jam’iyyar PDP da majalisar dattawa na cikin jerin waɗanda ake ƙara a shari’ar, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marvis Ossai ya bukaci kotun da ta soke takardar shaidar cin zaɓen Sanata Nwoko da kuma umartar INEC da ta gudanar da sabon zaɓe.

Har ila yau, ya bukaci kotun da ta umarci Sanata Nwoko ya mayar da duk albashi, alawus da duk wani kudin da ya karɓa tun daga Janairu 2025.

Ana so a hana sanatan takarar kowace kujera

Kari kan haka, ya nemi kotu da ta hana Sanata Nwoko tsayawa takara a kowace kujera har sai ya cika duk sharuɗɗan da hukuncin kotu za ta tanadar.

Mutumin ya ce tafiyar Nwoko zuwa APC ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, tunda babu rikici a PDP da zai iya zama dalilin barinsa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

A cikin takardar ƙarar, ya bayyana cewa Sanata Nwoko ya bar PDP a ranar 30 ga Janairu, duk da cewa ya samu kujerarsa ne a 2023 bisa tikitin jam’iyyar.

Ya kuma yi nuni da cewa sauya shekar Nwoko ya jawo wa PDP babbar asara a yankin, tare da rage wa jam’iyyar ƙarfi a siyasance.

Dan PDP ya fadi kuskuren sanata Nwoko

Sanata Ned Nwoko ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Abdullahi Ganduje, ya karbi Sanata Ned Nwoko da ya sauya sheka zuwa APC daga PDP. Hoto: @GovUmarGandujee
Asali: Twitter

Marvis Ossai ya ce idan ba a dakatar da wannan mataki ba, hakan zai ƙara ƙarfafa cin amanar jam’iyya da kuma rashin da’a a majalisa.

Dan mazabar ya bayyana cewa Sanata Nwoko yanzu yana wakiltar wata manufa daban da wacce suka zaɓe shi akanta a 2023.

Har ila yau, ya ce sauya shekar Nwoko na nufin yana goyon bayan jam’iyyar da ta yi yaki da PDP a 2023 domin hana shi cin zaɓe.

Marvis Ossai ya yi gargadin cewa lokaci na da matukar muhimmanci a wannan ƙara, don haka kotu ta hanzarta yanke hukunci don tabbatar da adalci.

Kara karanta wannan

Shari'ar Yahaya Bello: Jami'an EFCC dauke da makamai sun mamaye kotu a Abuja

Har zuwa yanzu, ba a mika shari’ar ga wani alkalin kotu don fara sauraron ƙarar ba.

'Abin da ya kamata su yi kenan' - Danja

Dalibin siyasa, Surajo Kasim Danja, ya ce abin da aka yiwa Sanata Nwoko shi ne ya fi dacewa ga 'yan siyasar da ke sauya sheka bayan sun ci zabe.

Dalibin siyasa, Surajo Kasim Danja, ya ce abin da aka yiwa Sanata Nwoko shi ne ya fi dacewa ga 'yan siyasar da ke sauya sheka bayan sun ci zabe.

A cewar Surajo Danja:

"Ba zai yiwu, jam'iyya ta bata lokacinta, da kudinta da sauran dabaeu don ganin ka ci zabe, amma ka zo ka canja jam'iyyar bayan ka ci zabe.
"Ba zai yiwu, jam'iyya ta bata lokacinta, da kudinta da sauran dabaeu don ganin ka ci zabe, amma ka zo ka canja jam'iyyar bayan ka ci zabe.
"Su al'ummarka sun zabe ka ne a karkashin jam'iyyar da ka tsaya takara, tare da yakinin za ka kare muradunsu. To amma sauya shekarka alama ce ta ba za ka ci gaba da kare muradunsu ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ministan Tinubu ya yi bayani kan barazanar ficewa daga APC

"Ya kamata dan siyasa ya sauya sheka ne kawai idan al'ummar da suka zabe shi ne suka ce ya canja. Ai wakili ne shi, don haka dole ya nemi amincewar wadanda yake wakilta."

Surajo Danja ya zargi mafi yawan 'yan siyasar da ke sauya sheka da bin muradun kansu, don cimma wani buri na kashin kansu, ba wai don al'ummarsu ba.

Sanata Nwoko ya ki karbar tayin kudi da mota

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa, ya yi magana kan tayin rufe baki da Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi masa.

Sanaya Nwoko ya bayyana cewa ba zai karɓi motar 'Land Cruiser' da Naira miliyan 10 a kowane wata daga gwamnan ba bayan ya sauka sheka zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.