Jam'iyyar APC Ta Yi Sabon Gwamna a Najeriya, Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki

Jam'iyyar APC Ta Yi Sabon Gwamna a Najeriya, Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki

  • An rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamna jihar Ondo bayan nasarar da ya samu a zaɓen da aka yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024
  • Gwamna Aiyedatiwa ya karbi rantsuwar kama aiki ne tare da mataimakinsa, Olayide Adelami a filin wasan Ondo da ke Akure yau Litinin, 24 ga watan Fabrairu
  • Gwamnan ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci, inda ya ce zai maida hankali kan fannonin ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Lucky Aiyedatiwa ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan Jihar Ondo bayan nasarar da ya samu a zaben da aka yi a 2024.

Rantsar da Gwamna Aiyedatiwa na nufin fara wa'adinsa na shekaru hudu bayan ya gaji marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu, wanda ya rasu a watan Disamba 2023.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa

Gwamna Aiedatiwa.
An rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, an rantsar da sabon gwamnan na APC ne a ranar Litinin, 26 ga Fabrairu, 2024, a filin wasan Ondo da ke Akure, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rantsuwa na zuwa ne bayan da Aiyedatiwa ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a watan Nuwamba a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Yadda aka rantsar da gwamna da mataimakinsa

An fara taron ne da rantsar da mataimakin gwamna, Olayide Adelami, wanda ya yi alkawarin gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da rikon amana.

Daga nan ne kuma aka rantsar da Gwamna Aiyedatiwa bayan ya yi rantsuwar yin adalci da bin kundin tsarin mulki sau da ƙafa da misalin karfe 12:59 na rana.

Bayan rantsuwar, sabon gwamnan ya zagaya filin wasan a cikin wata buɗaɗɗiyar mota, yana daga hannu ga magoya bayansa da suka cika wurin domin nuna goyon baya da taya shi murna.

Kara karanta wannan

Abba ya zama gwamnan gwamnonin Afrika, an gwangwaje shi a kasar waje

Dubban jama’a, ciki har da shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, da manyan baki daga sassa daban-daban na jihar da ƙasar baki ɗaya, sun halarci taron domin shaida wannan gagarumin bikin.

Sabon gwamnan Ondo ya ɗauki alƙawura

Aiyedatiwa ya yi alkawarin gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan ci gaban jihar Ondo.

Ya ce gwamnatinsa za ta fifita fannonin ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki, da samar da ayyukan yi ga matasa, rahoton The Nation.

Lucky Aiyedatiwa.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi alkawarin ɗaga darajar jihar Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Gwamna Aiyedatiwa ya kuma bayyana cewa zai gina kyakkyawar alaka da dukkan bangarorin shugabanci domin ci gaban Ondo.

Wannan rantsuwa na nuna cikar burin Aiyedatiwa na jagorantar jihar Ondo a hukumance, bayan da ya rike mukamin gwamna na rikon kwarya sakamakon rasuwar Akeredolu.

Yanzu dai an dora masa alhakin jagorancin jihar har zuwa 2028, tare da fatan zai cika alkawuran da ya dauka ga al’ummar Ondo.

Kara karanta wannan

An bankado umarnin Tinubu da zai illata Arewa, NARTO ta gargadi gwamnati

Gwamna Aiyedatiwa ya kori hadimai 2

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kori mata 2 daga cikin tawagar masu taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a.

Waɗanda korar ta shafa sun haɗa da babbar mataimakiya ta musamman kan bincike da rubuce-rubuce, Ewatomilola Emiola da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin kafafen sada zuminta, Kikelomo Isijola.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel