Dan Majalisa a Arewa Zai Hada kan Yarbawa a Yankin domin Zaben Tinubu a 2027
- Dan majalisar wakilai, Hon. Leke Abejide ya bukaci hadin kan Yarbawa a yankin kan zaben 2027
- Hon. Abejide ya bukaci shugabannin Yarbawa a Arewa su marawa Bola Tinubu baya a takararsa ta 2027 don ci gaban al'umma
- A taron cika shekara 10 na shugabannin gargajiya na Yarbawa a Arewa, Abejide ya jaddada muhimmancin hadin kai da gujewa siyasar rarrabuwar kawuna
- Ya kuma kaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 57.2 da gina fada na zamani a Kano domin karfafa tasirin Yarbawa da ci gaban al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar gwamna na ADC a Kogi, Hon. Leke Abejide, ya bukaci shugabannin Yarbawa a Arewa su marawa Tinubu baya a takararsa ta 2027.
Hon. Abejide wanda dan majalisar wakilai ne daga jihar Kogi ya ce hadin kai yana da matukar muhimmanci.

Asali: Facebook
Asiwajun Yarbawa a Kano ya magantu kan zabe
A taron cika shekara 10 na Kungiyar Sarakunan Gargajiya na Yarbawa a Arewa da FCT, Abejide ya bukaci hadin kai da gujewa siyasar rarrabuwar kawuna, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abejide wanda shi ne Asiwaju na Yarbawa a Kano, ya jaddada cewa hadin kan Yarbawa yana da matukar muhimmanci wajen samun tasiri a kasa da ci gaban al'umma.
“Yarbawa suna da yawa a Najeriya, idan aka cire su, giɓi zai bayyana sosai, don haka, dole mu kasance tare."
“Zan taimaka muku idan muka hada kai wajen goyon bayan Shugaban kasa, tasirinku a al'umma zai taimaka wajen cimma wannan buri."
- Hon. Leke Abejide
Dan Majalisa ya gina hanya a Kano
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Yagba, Abejide, ya ba da tabbacin goyon bayansa ga ci gaban kungiyar da bunkasa al'ummomin Yarbawa a Arewa.
Ya sanar da gina hanya mai tsawon kilomita 57.2 da kuma shirin gina fada na zamani a Kano don karfafa tasirin Yarbawa a Arewa.
Shugaban sabuwar kwamitin shugabanni, Muritala Adeleke, ya sha alwashin hada kan Yarbawa da bunkasa shirye-shiryen tattalin arziki ga al'ummomin Yarbawa a Arewa.
Dan Majalisa ya bukaci fassara kudirin haraji da Hausa
Kun ji cewa wani dan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Hon. Leke Abejide ya bukaci a fassara kudirin haraji zuwa harshen Hausa.
Hon. Leke ya shawarci fassara kudirin zuwa harshen Hausa duba da yadda matsalar ta fi yawa a Arewacin Najeriya saboda a fi fahimtar lamarin da kyau.
Asali: Legit.ng